Labarai

Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Guinea na nuni da cewa, ana zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar bayan da aka jiyo ƙazamar musayar wuta a Conakry, babban birnin ƙasar, a wannan Asabar ɗin. Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami'an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya, ba shiga ba fita. Wata majiya da aka sakaya sunanta ta ce, “Ana musayar wuta daga tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tare da harba makaman yaƙi a Kaloum." “Tun da asuba aka kulle garin, ba shiga, ba fita," in ji wani ɗan kasuwa a yankin. Guinea na ɗaya…
Read More
Gwamnan Zamfara ya karɓo wa ‘yan gudun hijira a jiharsa tallafin gaggawa

Gwamnan Zamfara ya karɓo wa ‘yan gudun hijira a jiharsa tallafin gaggawa

Daga BASHIR ISAH Nan ba da jimawa ba 'yan gudun hijira da ma waɗanda rikici ya ɗaiɗaita a Jihar Zamfara za su dara, biyo bayan tallafin da Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya karɓo musu daga Gwamnatin Tarayya. Tallafin gaggawar ya ƙunshi buhunan shinkafa, katan-katan na spaghetti, garin semovita, kayan aikin gona, kekunan ɗinki, kwamfutoci, litattafan rubutu da dai sauransu. A ranar Alhamis da ta gabata Gwamna Lawal ya kai ziyara Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira da Waɗanda Rikici ya Ɗaiɗaita ta Ƙasa don kyautata danganta da kuma nema wa 'yan gudun hijira a jiharsa tallafi kamar yadda mai magana…
Read More
Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin harin ta’addanci a Kano

Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin harin ta’addanci a Kano

Daga BASHIR ISAH Jami'an tsaro a Jihar Kano sun samu nasarar daƙile yunƙurin harin ta'addanci da Boko Haram ta shirya kaiwa a yankin Ƙaramar Hukumar Gezawa a jihar. Sojoji da DSS ne suka daƙile wannan yunƙuri a ranar Juma'a, tare da kama wasu mutum biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne. Cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun sojoji, Onyema Nwachukwu ya lissafo wasu makamai da suka ƙwace da suka haɗa da bindiga ƙirar AK 47 guda biyar, bindigar harba roka ɗaya, bom samfurin RPG guda shida, rigunan aiki na sojoji da dai sauransu. Sanarwar ta ƙara da…
Read More
Atisaye: Babu buƙatar jama’a su tada hankulansu – NAF

Atisaye: Babu buƙatar jama’a su tada hankulansu – NAF

Rundunar Sojan Sama (NAF) ta yi kira ga 'yan ƙasa kan cewa kada su firgita ko tada hankalinsu da ganin jami'anta bajaja a kan hanyoyi a sassan ƙasa a ranar Asabar. Daraktan Yaɗa Labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, gudun sassarfa na shekara-shekara na tsawon kilomita 10 da suka saba yi, na bana zai gudana ne a ranar Asabar, 4 ga Nuwamban 2023 da misalin ƙarfe 6.00 a Abuja da sauraran sassan ƙasa inda ake da sansanonin rundunar. Sanarwar ta ce, “Ana shawartar al'umma musamman masu abubuwan hawa da waɗanda ke zama…
Read More
Ƙaramin kasafin kuɗi: Sojojin ruwa sun shafa wa Tinubu kashin kaji

Ƙaramin kasafin kuɗi: Sojojin ruwa sun shafa wa Tinubu kashin kaji

*Ban buƙaci yin ta-more ba, inji Shugaban Ƙasa*Majalisa ta fizgo wa ɗalibai biliyan N5 daga Fadar Shugaban Ƙasa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daga dukkan alamu wani ɓangare na ƙaramin kasafin kuɗin da Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya ta nemi a ba ta cikin ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na 2023, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa Majalisar Dokoki, domin neman amincewarta, ya nemi ya shafa shugaban kashin kaji a wajen akasarin masu sharhi da lura da al’amuran yau da kullum a faɗin ƙasar, saboda yadda cece-kuce ya ɓarke akan batun har ma Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu kan lamarin. Wannan…
Read More
Ministoci mata na Tinubu suna bayyana jiki kamar masu takarar sarauniyar kyau, inji ministan Buhari

Ministoci mata na Tinubu suna bayyana jiki kamar masu takarar sarauniyar kyau, inji ministan Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Ministan Sadarwa a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Adebayo Shittu ya soki ministoci mata a majalisar ministocin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa su na saka sutura tamkar ’yan takara sarauniyar kyau. Shittu ya bayyana ra’ayinsa ne a yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada muhimmancin jami’an gwamnati su tunkari ayyukansu da muhimmanci. Shittu, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2019, ya yi waɗannan kalamai ne a matsayin martani ga jawabin da shugaba Tinubu ya…
Read More

’Yan Nijeriya sun san ’yan siyasa ɓarayi ne amma su na zaɓen su – Amaechi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cikin wani faifen bidiyo da aka yaɗa a shafin ‘X’ (Tiwita a da) na gidan talabijin na Channels TV, Mista Rotimi Amaechi, fitaccen ɗan siyasa, tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin da ta gabata, ya yi wata magana mai zafi game da tunanin masu zaɓe a Nijeriya. Kalaman Amaechi sun nuna abin da yake ganin tamkar rashin tunani ne a tsakanin ’yan Nijeriya dangane da mutuncin ’yan siyasar ƙasar, inda ya ce, duk ’yan ƙasar na matuƙar zargin ’yan siyasa da zama ɓarayin gwamnati, amma ba su fasa zaɓen su ba.…
Read More
Boko Haram na iya shafe Nijeriya idan ba a tashi tsaye ba – Zulum

Boko Haram na iya shafe Nijeriya idan ba a tashi tsaye ba – Zulum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi gargadin cewa rikicin Boko Haram na iya shafe ƙasar nan idan ba a tashi tsaye don shawo kan shi ba. Ya yi gargaɗin ne lokacin da yake jawabi bayan ya karɓi baƙuncin kwamitin gudanarwa na Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) a zauren majalisar dokokin jihar da ke Maiduguri a ranar Litinin. Ya ce, “Matsayin Jihar Borno a taswirar Nijeriya yana da matuƙar muhimmanci a gare mu baki ɗaya. Jihar Borno tana da iyaka da Chadi, Kamaru, da Jamhuriyar Nijar. Iyakokinmu sun yi yawa don haka…
Read More
Ma’aikatan lantarki sun umarci mambobinsu su janye ayyukansu bayan jikata shugaban NLC

Ma’aikatan lantarki sun umarci mambobinsu su janye ayyukansu bayan jikata shugaban NLC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ma’aikatan wutar lantarki a ƙarƙashin Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) sun buƙaci mambobinsu da su dakatar da dukkan ayyukansu a faɗin ƙasar nan da tsakar daren Alhamis. Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne domin nuna rashin amincewarta da kama tare da cin zarafin da ‘yan sanda suka yi wa Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, Joe Ajaero a ranar Laraba a wani gangamin zanga-zanga a Owerri, babban birnin jihar Imo. Biyo bayan harin da jami’an tsaro suka kai wa Ajaero a jihar Imo, NLC ta ce shugabannin qungiyoyin ƙwadagon za su yi…
Read More
A gaggauta kawo ƙarshen satar ɗaliban sakandare a Arewa – Talatu ‘Yar Nijeriya

A gaggauta kawo ƙarshen satar ɗaliban sakandare a Arewa – Talatu ‘Yar Nijeriya

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Jarumar Hausawan Duniya, Hajiya Talatu Suleiman 'Yar Nijeriya, ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da cewa a gaggauta kawo ƙarshen satar ɗaliban sakandare da ya zama ruwan dare a yankin Arewacin Nijeriya. Hajiya Talatu 'Yar Nijeriya ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron manema labarai da ta kira inda ta ja kunnen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da cewa ba za su lamunci yawan kai hare-hare da ake yi makarantun sakandare ana sace ɗalibai mata ba. Ta ce a matsayinta na uwa kuma Basarakiya a Ƙungiyar Hausawa ta Duniya shi ya sa…
Read More