Labarai

’Yan bindiga sun yi awon gaba da malami a motar gawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani malamin addinin Islama, Alfa Fasasi Ola Mejabi da ƙaninsa a Jihar Kogi. Malamin da sauran su su na miƙa ɗauke da gawar babban Limamin Ayegunle Gbede, Sheikh Musa Olorunkemi, daga Lokoja zuwa Ayegunle Gbede da ke ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi domin yi masa jana’iza a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi karo da masu garkuwa da mutane. Ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin motar da suka tsallake rijiya da baya ya shaida wa manema…
Read More
Tinubu ya cire FCT daga tsarin Asusun Bai-ɗaya, ya ƙarfafa Wike kan tara kuɗin shiga

Tinubu ya cire FCT daga tsarin Asusun Bai-ɗaya, ya ƙarfafa Wike kan tara kuɗin shiga

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cire Hukumar Birnin Tarayya FCTA daga tsarin Asusun Bai-ɗaya (TSA). Shugaban ya ce ɗaukar wannan mataki zai ƙarfafa wa Ministan Abuja, Nyesom Wike wajen sarrafa kuɗin shigar da Abuja ke tarawa yadda ya kamata wajen bunƙasa birnin. Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma'a, Wike ya ce Tinubu ya amince da ƙirƙiro Hukumar Kula da Ma'aikata ta Abuja. Ya ce yin haka zai bada damar cigaban ma'aikatan FCT. Kafin wannan lokaci ma'aikatan yankin Abuja na kokawa kan rashin wannan hukuma wadda za ta kula musu da cigabansu a bakin aiki.
Read More
Ya binne ƙaninsa da ransa kan satar Naira 1,000 a Kogi

Ya binne ƙaninsa da ransa kan satar Naira 1,000 a Kogi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Larabar da ta gabata ne al’ummar Apamisede da ke Ƙaramar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi suka shiga ruɗani yayin da aka binne wani yaro ɗan shekara takwas da ransa sakamakon satar kuɗi naira dubu ɗaya kacal (N1000) mallakin mahaifiyarsa. A cewar shaidar gani da ido, mahaifiyar yaron ta umurci babban ɗanta mai shekaru 19 da ya hukunta yaron saboda satar kudin. Babban yaya wajen aiwatar da umarnin mahaifiyarsa, ya yanke shawarar binne yaron da ransa har sai da makwabta nagari suka kawo masa ɗauki suka tono yaron da ke numfashi da ƙyar. Jami’in hulɗa…
Read More

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 50, sun kama 114 a mako guda – Hedkwatar Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hedikwatar tsaro ta ce sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda 50 tare da kame wasu 114 cikin mako guda a hare-hare daban-daban a yankin Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa maso Yamma. Darakta mai kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar, ranar Alhamis a Abuja. Mista Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 49 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda. Ya ce dakarun Operation Haɗin Kai da…
Read More
Gobe za a ƙaddamar da littafin ‘100+ questions before Nikkah’

Gobe za a ƙaddamar da littafin ‘100+ questions before Nikkah’

Daga AISHA ASAS Shahararriya kuma ƙwararriyar mai bayar da shawarwari kan zamantakewar aure da kuma rayuwa bakiɗaya, Khadija Ibrahim, marubuciya da ta jima tana gyara al'umma da alƙalaminta, ta shirya tsaf don bayar da ƙarin gudunmawa ga masu shirin yin aure, wato littafin da zai amsa tambayoyi ɗari har da ɗori da mata da maza suke buƙatar sani kafin su shige daga ciki. Littafin mai suna tambayoyi ɗari da ɗori kafin aure, wanda zai kasance a turance, wato '100+ questions before Nikkah' zai amsa kusan dukkan tambayoyin da ake buƙatar sani game da aure, waɗanda za su fitar da samari…
Read More

Tsohon Ministan Cikin Gida, Sanata Bello Maitama ya kwanta dama

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Bello Maitama Yusuf, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 76. Wani na kusa da marigayin, Hussaini Dalhatu, shi ne ya tabbatar da rasuwar nasa a ranar Juma'a. Ya ce za a yi jana'izar Sardauna Dutse a fadar Sarkin Kano bayan an sauko daga Juma'a. A halin rayuwarsa, marigayin ya yi sanata daga shekarar 1999 zuwa 2007. Kuma ya riƙe muƙamin Ministan Harkokin Cikin Gida a 1981, sannan Ministan Kasuwanci 1982. An haifi Bello Maitama Yusuf ne garin Gwaram, Jihar Jigawa a shekarar 1947.
Read More
Gwamnan Zamfara ya yi kira ga malamai kan riƙo da gaskiya

Gwamnan Zamfara ya yi kira ga malamai kan riƙo da gaskiya

*Ya jaddada aniyarsa kan ƙaurace wa sulhu da 'yan bindiga A yau Juma’a, Gwamnan Dauda Lawal, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ƙauracewa duk wani batun sulhu da ɓarayi a faɗin Jihar Zamfara. Gwamnan Ya bayyana haka ne a yayin da ya halarci taron wa’azi na mako-mako da aka saba gudanarwa a Gusau, inda ya hori Malaman Addini da su kasance masu riƙo da gaskiya. Wata takardar sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce wannan taron wa’azin mako an kwashe shekaru ana gudanar da shi, kuma wannan shi ne karo na 1,…
Read More
Ana nuna damuwa kan yadda Tinubu ba ya kiran Zaman Majalisar Zartarwa

Ana nuna damuwa kan yadda Tinubu ba ya kiran Zaman Majalisar Zartarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai kira taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya ba kwanaki 44 da kammala zaman majalisar da aka gudanar a ranar 28 ga watan Agusta. Hakan ya cigaba da haifar da ayar tambaya kan ko hakan na iya shafar harkokin mulki ko a'a? Majalisar Zartaswa ta Tarayya, wadda shugaban ƙasa ke jagoranta, ita ce Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya kuma wani ɓangare na zartarwa. Matsayin tsarin mulki na FEC, kamar yadda yake ƙunshe a cikin Dokar Ayyuka na Ministoci, ita ce ta zama ƙungiya mai ba da shawara ga shugaban ƙasa. A…
Read More
EFCC ta ƙwato sama da Naira Biliyan 27 a hannun tsofaffin gwamnoni da ministoci

EFCC ta ƙwato sama da Naira Biliyan 27 a hannun tsofaffin gwamnoni da ministoci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta Nijeriya ta bayyana cewa, ta ƙwato jimillar Naira 27,184,357,524.52 da dala 19,084,419.33 a wasu shari’o’i uku na karkatar da kuɗaɗe. Daga cikin wannan adadin da aka ƙwato, an gano Naira biliyan 12.7 ne daga hannun mutum ɗaya. Hukumar ta EFCC na binciken tsaffin gwamnoni da tsofaffin Ministoci da wasu jami’an gwamnati a faɗin ƙasar nan a ƙoƙarin da ta ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa. Muƙaddashin shugaban hukumar ta EFCC Abdukarim Chukkol ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai…
Read More
Hukumar Alhazai ta bai wa maniyyata wa’adin makonni uku su fara adashin gata

Hukumar Alhazai ta bai wa maniyyata wa’adin makonni uku su fara adashin gata

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta ce, hukumar na da tsawon makonni uku domin tattaunawa da masu yi wa alhazai hidima a ƙasar Saudiyya, inda ta buƙaci maniyyatan Nijeriya da su fara ajiye Naira miliyan 4.5 kafin lokacin aikin hajjin a matsayin adashin gata. Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ta ce Masarautar ta sanya ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023 don kammala taron share fage da masu ba da hidima, inda ta ce, kafin nan ya kamata hukumar ta yi kiyasin aniyar maniyyata aikin…
Read More