Labarai

Allah Ya yi wa Jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola asuwa

Allah Ya yi wa Jarumar Kannywood, Hajiya Binta Ola asuwa

Daga UMAR GARBA a Katsina Allah Ya yi wa shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Hajiya Binta Ola rasuwa. Hajiya Binta ta rasu ne da misalin ƙarfe 3 na daren jiya Talata, a gidanta dake Sabuwar unguwa Ƙofar Ƙaura, dake jihar Katsina bayan gajeruwar rashin lafiya. Majiyar mu ta ce za a yi jana'izar marigayiyar a wannan Laraba da misalin ƙarfe 10 na safe a gidanta dake Sabuwar unguwa cikin garin Katsina.
Read More
Dalilin da ya sa na tsunduma siyasa duk da kasancewa ta limamin coci – Mawaƙi Banky W 

Dalilin da ya sa na tsunduma siyasa duk da kasancewa ta limamin coci – Mawaƙi Banky W 

Daga AISHA ASAS  Shahararren mawaƙin Nijeriya Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W, ya bayyana dalilin sa na shiga siyasa har ya tsaya takara, duk da cewa, a yanzu shi limami ne na Coci. A cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mawaƙin wanda a halin yanzu yake jagorantar wata Coci ya bayyana cewa, ya shiga harkar siyasa ne don ya canza ma'anar da mutane da yawa suke yi wa siyasa, inda suke kallon dukka wani ɗan siyasa a matsayin mutumin banza. Mawaƙin ya ce, shigar tasa siyasa har ya tsaya takara, zai zama wata ishara da…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 62 ne za su amfana da shirin ‘cash transfer’ – Betta Edu

‘Yan Nijeriya miliyan 62 ne za su amfana da shirin ‘cash transfer’ – Betta Edu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, 'yan Nijeriya miliyan 62 ne za su amfana daga shirin ba da tallafi na "Conditional Cash Transfer" inda kowanne zai riƙa samun tallafin kuɗi na N25,000 duk wata har na tsawon wata uku. Kazalika, gwamnatin ta yi alkawarin tallafa wa mata 'yan kasuwa su miliyan ɗaya da rabi ta shirin "Iyaloja Fund". Ministar Jinƙai da Yaƙi da Talauci, Dr Betta Edu ce ta bayyana haka sa'ilin da ta kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ziyara ranar Talata a ofishinsa da ke Abuja. A cewarta, “Za mu aiwatar da…
Read More
Muƙamin Minista: Tinubu ya maye gurbin El-Rufai da Balarabe

Muƙamin Minista: Tinubu ya maye gurbin El-Rufai da Balarabe

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya zaɓi Abbas Balarabe don maye gurbin tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin minista. Hakan na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talata Haka nan, Dr Jamila Ibrahim da Ayodele Olawande na daga cikin sunayen da wasiƙar ta ƙunsa wanda Tinunu ke neman majalisar ta tabbatar da su a matsayin ministocin matasa. Idan ba a manta ba, a watan Agustan da ya gabata Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da ministoci 45, amma ta ƙi tabbatar da wasu uku, ciki har da toshon Gwamnan…
Read More
Hon. Hassan El Ben Jaz ya raba wa mutum 3210 tallafin abinci a Yobe

Hon. Hassan El Ben Jaz ya raba wa mutum 3210 tallafin abinci a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu A yunƙurin sa wajen rage wa al'ummar mazaɓarsa wahalhalun da cire tallafin man fetur ya jefa jama'a, ɗan majalisa a Mazaɓar Bade/Jakusko a jihar Yobe, a zauren majalisar wakilai ta ƙasa, a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Hon. Hassan Jakduwa KaiKaku (El Ben Jaz) ya ƙaddamar da rabon kayan abinci, tare da takin zamani ga manoma a mazaɓarsa dake jihar Yobe. A jawabinsa wajen ƙaddamar da rabon kayan a Gashuwa, Hon. Hassan El Ben Jaz, wanda Malam Salisu Jawi ya wakilta a taron, ya ce aƙalla mutum 3210 ne a mazaɓarsa za su ci gajiyar tallafin a…
Read More
Ba duk finafinan Nollywood ne ake iya hasashen ƙarshensu ba – Tana Adelana

Ba duk finafinan Nollywood ne ake iya hasashen ƙarshensu ba – Tana Adelana

Daga AISHA ASAS  Jaruma a masana'artar finafinai ta Kudu, Tana Adelana ta musanta faɗar mutane da suke cewa, dukka finafinan da masana'antar Nollywood ke fitarwa mai kallo zai iya hasashen yadda zaren labarin zai ci gaba har ya zuwa ƙarshe.  Jarumar ta mayar da martani da cewa, ba fa kowanne fim daga cikin finafinan Nollywood ne mai kallo zai iya hasashen yadda labarin zai ci gaba, domin akwai waɗanda sai dai mai karatu ya tsumayi zuwan ci gaba, wanda zai zo masa a ba yadda ya yi tunanin sa ba. A cikin tattaunawar ta a shirin Saturday Beats, jaruma Tana,…
Read More
Rushewar ginin coci ta yi ajalin Fasto a Binuwai

Rushewar ginin coci ta yi ajalin Fasto a Binuwai

Bayanin da muka samu yanzu-yanzu ya ce, sashen ginin Cocin Dunamis da ke daura da Mission Ward North Bank a Makurɗi, babban birnin Jihar Binuwa, ya rushe. Blueprint Manhaja ta kalato cewar, rushewar ginin wadda ta auku da safiyar wannan Talatar ta yi ajalin wani fasto tare da jikkata wasu masu ibada a mujami'ar. Bayanai sun ce, Faston tare da wasu mutum uku na tsaka da gabatar da addu'a ne a lokacin da wani ɓangaren ginin ya rikito a kansu. Ya zuwa haɗa wannan labari babu cikakken bayani kan dalilin aukuwar iftila'in. Da aka nemi jin ta bakinta, Kakakin 'yan…
Read More
DSS sun cafke budurwar da ta yi wa Shettima da Gawuna barazanar ƙunar baƙin-wake

DSS sun cafke budurwar da ta yi wa Shettima da Gawuna barazanar ƙunar baƙin-wake

Jami'an DSS a Kano sun cafke Fiddausi Ahmadu, 'yar shekara 23, bayan da ta yi barazanar ƙunar baƙin-wake a kan waɗanda ta ce suna da hannu a nasarar da Jam'iyyar APC ta samu a shari'ar zaɓen gwamnan Kano a Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe. Majiya mai tsushe ta tabbatar wa jaridar News Point Nigeria da batun kama budurwar da DSS ta yi da safiyar Talata. Majiyar ta ce Fiddausi na iƙirarin taya Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusu da jam'iyyarsa ta NNPP faɗa ne kamar yadda aka gani a cikin wani faifan bidiyon da aka yaɗa. An ji Fiddausi a cikin bidiyon…
Read More
Ƙungiyoyin ƙwadago sun jinginar da aniyar shiga yajin aiki, yayin da ƙarin albashi na N35,000 zai fara aiki daga Satumba

Ƙungiyoyin ƙwadago sun jinginar da aniyar shiga yajin aiki, yayin da ƙarin albashi na N35,000 zai fara aiki daga Satumba

Ƙungiyar ƙwadago NLC da takwararta TUC, sun jinginar da aniyarsu ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani na tsawon wata guda. Hakan na ƙunshe ne cikin takardar yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ɓangaren gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin a taron da suka yi ranar Litinin. Yayin zaman nasu, Gwamnatin Tarayya ta yi tayin ƙarin albashi na N35,000 amma ga ma'aikatanta kaɗai wanda zai fara aiki daga watan Satumba zuwa lokacin da za a rataɓɓa hannu kan sabon mafi ƙarancin albashi. Tuni dai sugabannin ƙungiyar Maritime Workers Union of Nigeria (MWUN) suka umarci mambobinsu da su koma bakin a tashoshin jirgin ruwan da ke…
Read More
Dangut ya zama Shugaban WAEC na ƙasa

Dangut ya zama Shugaban WAEC na ƙasa

An naɗa Dokta Amos Dangut a matsayin sabon Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Afrika ta Yamma (WAEC) a Nijeriya. Kafin naɗin nasa, Dangut shi ne Mataimakin Rijistara na WAEC na ƙasa. Naɗin nasa ya biyo bayan ƙarewar wa'adin aikin Mr Patrick Areghan a matsayin shugaban hukumar na ƙasa. Bayanin naɗi na ƙunshe ne cikin sanarwar da WAEC ta fitar ranar Litinin ta bakin Mrs Moyosola Adesina wadda ta kasance Muƙaddashin Shugaban Sashen Hulɗa da Jama'a hukumar a Legas. Adesina ta bayyana cewa, Dangut ya fara aiki da hukumar ne a shekarar 1998 ne a matsayin "Assistant Registrar (AR)…
Read More