04
Jun
Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Progressives Congress (APC) Defense Coalition na babban zaɓen 2023 ta yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara, Lawal Dauda da ya maida hankali wajen yi wa jihar aiki maimakon ɓata lokaci wajen faɗa da tsohon Gwamnan jihar, Bello Matawalle. Ƙungiyar ta ce Bello ya bar Naira biliyan 2.5 a asusun jihar, kuma ya taɓuka wajen tattalin kadarorin jihar da ma fannin tsaro don amfanin jihar baki ɗaya. Ta ƙara da cewa, iƙirarin da Dauda ya yi kan cewa tsohon Gwamnan bai bar komai a asusun jihar ba, hakan wani yunƙuri ne na hana a yi wa tsohon…
