Labarai

CBN ya ƙaryata iƙirarin rage darajar Naira akan Dala

CBN ya ƙaryata iƙirarin rage darajar Naira akan Dala

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Bankin Najeriya CBN ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya rage darajar Naira zuwa kusan Naira 630 akan dala. Tun da farko dai rahoton faɗuwar darajar kuɗin ne ɗaya daga cikin jaridun ƙasar ta ruwaito. Sai dai a wata sanarwa a ranar Alhamis, muƙaddashin shugaban sashen sadarwa na bankin, Dr Isa Abdulmumin, ya bayyana hakan a matsayin ƙarya. “Rahoton labarai, wanda a tunanin jaridar ya keɓanta, cike yake da ƙarya da ɓatanci, wanda ke nuna yiwuwar jahilci da gangan game da yadda kasuwar canji ta Nijeriya ke aiki,” inji shi.…
Read More
Sarkin Musulmi ya ƙarfafi Qausain TV su ƙara himma

Sarkin Musulmi ya ƙarfafi Qausain TV su ƙara himma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya shawarci Kamfanin Talabijin na Qausain TV da ya ruvanya ƙoƙarinsa wajen isar da saƙo ga al'umma. A ziyarsar da Qausain TV ƙarƙashin jagorancin Shugaban Tashar, Nasir Musa Albanin Agege a fadar Sarkin Musulmin, ta ƙunshi wasu daga cikin shugabannin kamfanin da suka haxa da Auwal MB, Hashim Abubakar Musa, Khalifa Muhammad Babandede da kuma Hassan Haruna. Bayan kyakkyawar tarba da tawagar ta samu, kazalika Sarkin Musulmin ya bulaci Qausain TV da ya ci gaba da aiki tuƙuru bisa ƙwarewa da sanin makamar aiki kamar yadda aka…
Read More
Tinubu ya naɗa Gbajabiamila Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu ya naɗa Gbajabiamila Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa

*George Akume ya zama Sakataren Gwamnatin Tarayya Daga BASHIR ISAH Shuganan Ƙasa Bola Tinubu, ya naɗa Shugaban Majalisar Wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa. Yayin da ya naɗa tsohon Gwamnan Jihar Binuwai kuma tsohon Ministan Ayyuka na musamman, George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Tinubu ya yi naɗe-naɗen ne a ranar Juma’a, inda tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya samu muƙamin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa. Bayanin naɗe-naɗen na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa-hannun Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Abiodun Oladunjoye. A…
Read More
A daina fargaba mu na da wadataccen mai – NNPCL

A daina fargaba mu na da wadataccen mai – NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yayin da aka fara dogayen layuka a gidajen mai a wasu sassa na Nijeriya bayan sanarwar cire tallafin mai da sabon Shugaban Ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai yi, kamfanin mai na NNPCL, ya ce jama’a su daina fargaba domin akwai wadataccen mai a ƙasa. Shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari, ya shaida wa BBC cewa, akwai mai don haka babu wata matsala da ya ke gani za a iya fuskanta da ta shafi qarancin mai. "Dama duk lokacin da aka samu irin wannan jawabi daga shugabanni, sai mutane su yi ta tururuwa suna…
Read More
Koya wa matasa sana’o’i zai ba su damar dogaro da kai – Wasila Aybo

Koya wa matasa sana’o’i zai ba su damar dogaro da kai – Wasila Aybo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Mai kamfanin 'Wasila Aybo General Enterprises' ta bayyana cewa abinda ya ja hankalinta wajen koya wa matasa sana'o'i shine duba da halin da al'umma suke ciki musamman matasa na rashin abin yi. Hajiya Wasila Shu'aibu Aybo ta bayyana hakan ne a taron yaye mutum 174 da aka koya wa sana'o'i ƙarƙashin tsarin Kwankwasiyya. Ta qara da cewa yadda matasa suka zama zauna-gari-banza da yawan mace-macen aure da iyaye maza da ke mutuwa a bar mata da marayu shi ya sa suke koya musu sana'o'i su samu abin yi da za su kula da kan su…
Read More
Sababbi da tsofaffin gwamnoni sun kai wa Buhari ziyarar ban-gajiya

Sababbi da tsofaffin gwamnoni sun kai wa Buhari ziyarar ban-gajiya

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata ƙasaitacciyar tawaga da ta ƙunshi gwamnoni masu ci da kuma tsofaffi, ta kai wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban-gajiya a mahaifarsa dake Daura ta Jihar Katsina a jiya Alhamis, 1 ga Yuni, 2023. Daga cikin gwamnonin akwai sabon gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, Dapo Abiodun na Jihar Ogun, Babajide Sanwo Olu na Jihar Legas, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Bala Muhammad na Jihar Bauchi, Hope Uzodinma na Jihar Imo da mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam. A sanarwar da ofishin babban mataimaki na musamman akan kafafen yaɗa labarai na zamani ya fitar,…
Read More
Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga sassan Nijeriya sun ce, a halin da ake ciki farashin fetur ya ƙaru zuwa Naira 700 kan kowace lita a wasu sassan ƙasar. Wannan ya biyo bayan sanar da cire tallafin mai baki ɗaya da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawbinsa ga ‘yan ƙasa jim kaɗan da rantsar da shi a ranar Litinin da ta gabata. Binciken Manhaja ya gano cewar, matakin cire tallafin da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya haifar da ƙarin farashin mai da kashi 100 zuwa 250, inda a yanzu ake sayar da lita guda na fetur tsakanin…
Read More
Katsinawa sun roƙi ‘yan Nijeriya a kan su yafe wa Buhari

Katsinawa sun roƙi ‘yan Nijeriya a kan su yafe wa Buhari

Daga UMAR GARBA a Katsina Al'ummar jihar Katsina sun roƙi 'yan Nijeriya da su yafe wa tsohon Shugaban Ƙasar, Muhammadu Buhari, a kan kura-kuran da ya aikata lokacin da yake kan mulki. Majiyar Manhaja ta ce, Katsina sun yi wannan roƙo ne a wajen taron hawan daushe na musamman da suka shirya wa Buhari s ranar Talata don karrama dawowarsa gida. Taron wanda Masarautar Daura ta shirya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Daura, Umar Faruq Umar, don maraba da dawowa gida ga Buhari bayan shafe shekara takwas yana mulkin ƙasar. A zantawarsu da manema labarai, Lawal Ado da Umaru Yusuf sun nuna…
Read More
HOTUNA: Yadda aka shirya wa tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari hawan daushe a Daura

HOTUNA: Yadda aka shirya wa tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari hawan daushe a Daura

Daga SANI MAIKATANGA Masarautar Daura a Jihar Katsina, ta shirya hawan daushe na musamman domin karrama dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida. Bikin ya gudana ne a ranar Talata tare da samun dandazon mahalarta. Buhari ya koma mahaifarsa Daura bayan kammala wa'adin mulkinsa a matsayin Shugaban Ƙasar Nijeriya a ranar 29 ga Mayu, 29. Ga ƙarin hotuna daga wajen taron:
Read More
Sabon Gwamnan Sakkwato ya soke naɗe-naɗen da Tambuwal ya yi gab da saukarsa

Sabon Gwamnan Sakkwato ya soke naɗe-naɗen da Tambuwal ya yi gab da saukarsa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Sa'o'i 24 shan rantsuwa Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Ahmad Aliyu ya soke naɗe-naɗen da gwamnatin Aminu Tambuwal ta yi da ƙarin girma ga ma'aikatan jihar bayan 19 ga watan Maris, 2023. Bayan haka, Gwamna Ahmad ya soke dukkanin canza sunayen manyan makarantun jihar da duk abin da ke da alaƙa da shugabannin gudanarwar makarantun, kamar yadda bayanin ya ce dukkaninsu, sun koma sunayensu da aka sansu da su a baya. A bayanin da ya yi wa manema labarai, kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya ce, Gwamnan ya ce za a sake wewayar naɗe-naɗen sarautun da tsohon…
Read More