Cire Tallafin Mai: Farashin fetur ya cilla zuwa N700 kan lita guda

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga sassan Nijeriya sun ce, a halin da ake ciki farashin fetur ya ƙaru zuwa Naira 700 kan kowace lita a wasu sassan ƙasar.

Wannan ya biyo bayan sanar da cire tallafin mai baki ɗaya da sabon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawbinsa ga ‘yan ƙasa jim kaɗan da rantsar da shi a ranar Litinin da ta gabata.

Binciken Manhaja ya gano cewar, matakin cire tallafin da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya haifar da ƙarin farashin mai da kashi 100 zuwa 250, inda a yanzu ake sayar da lita guda na fetur tsakanin N500 zuwa N700 a wasu sassan ƙasar.

Da yake jawabi a ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya ce masu ido da kwalli su suka fi cin gajiyar tallafin na mai fiye da talakawa shi ya sa ya ga dacewar cire tallafin baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, za a karkatar da kuɗaɗen tallafin man wajen samar da ababen more rayuwa don amfanin al’ummar ƙasa baki ɗaya.