Katsinawa sun roƙi ‘yan Nijeriya a kan su yafe wa Buhari

Daga UMAR GARBA a Katsina

Al’ummar jihar Katsina sun roƙi ‘yan Nijeriya da su yafe wa tsohon Shugaban Ƙasar, Muhammadu Buhari, a kan kura-kuran da ya aikata lokacin da yake kan mulki.

Majiyar Manhaja ta ce, Katsina sun yi wannan roƙo ne a wajen taron hawan daushe na musamman da suka shirya wa Buhari s ranar Talata don karrama dawowarsa gida.

Taron wanda Masarautar Daura ta shirya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Daura, Umar Faruq Umar, don maraba da dawowa gida ga Buhari bayan shafe shekara takwas yana mulkin ƙasar.

A zantawarsu da manema labarai, Lawal Ado da Umaru Yusuf sun nuna farin cikinsu ganin cewa Buhari ya kammala mulki lafiya ya kuma dawo gida ƙalau.

Umaru ya ce “Buhari mutumin kirkiri. Ya yi mana aiki muna matuƙar farin ciki. Saboda haka lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su yafe masa”.

Hawan dabar ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da sabon Gwamnan Katsina, Dikko Raɗɗa, Gwamnan Borno, Babagana Zulum, Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman, tshohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari da sauransu.