Na yi kuka da aka ce Sanata Binani ta faɗi zaɓe – Aisha Gombe

“Mata ‘yan siyasa na shan tsangwama a tsakanin al’umma”

“Soyayyar Buhari ce ta sa na shiga siyasa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Mata a kowanne mataki suna ba da gagarumar gudunmawa wajen harkokin raya ƙasa da cigaban dimukraxiyya. Ana iya ganin mata a ko’ina yayin da aka ce an buga gangar siyasa, inda za a yi ta faɗi tashi tare da su da sauran ýan ƙasa wajen neman goyon baya ga ýan takarar su da jam’iyyunsu na siyasa. Hajiya Aisha Usman Ahmad na daga cikin waɗannan jajirtattun mata da suke taka rawar gani a siyasar Jihar Gombe da ma Nijeriya bakiɗaya. A zantawarta da wakilin jaridar Manhaja, wannan ýar siyasa, basarakiya kuma ýar kasuwa ta bayyana yadda za ta yi kewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda a dalilinsa ta fara shiga harkokin siyasa, da kuma ƙwarin gwiwar da take da shi kan sabon zaɓaɓɓen shugaban qasa Bola Ahmed Tinubu.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

HAJIYA AISHA: Salamu alaikum. Sunana Hajiya Aisha Usman Ahmad, Sarauniyar Farang Malabu kuma Majidaɗin Jarumar Kaltungo. Ni ýar siyasa ce, kuma ina tava harkokin kasuwanci. Ni ce kuma shugabar ƙungiyar mata masu marawa zaɓaɓɓen shugaban Nijeriya baya ta The Champ Supporters for Jagaban a Jihar Gombe. Har wa yau kuma na jagoranci qungiyar mata da ta tallafa wa sake zaven Gwamnan Jihar Gombe, ɗan Majen Gombe na farko, Muhammadu Inuwa Yahaya, ta Inuwa 4+4, duk da ni aka yi yaqin neman zaɓen su. Ina kuma da aure da yara.

Menene tarihin rayuwarki, a taƙaice?

Ni asalina daga Qaramar Hukumar Fufore ne a Jihar Adamawa, kuma ni Bafulanatana ce. A nan aka haife ni, kuma a nan na tashi har na yi karatuna na firamare har zuwa sakandire. Daga nan ne kuma aka yi min aure, na dawo da zama nan Gombe tare da maigidana, har Allah Ya yi mana arziƙin haihuwar ýaýa biyar da jikoki huxu. Na koma makaranta a nan Gombe inda na shiga Gombe Academy, kuma har na yi karatun addini a nan Higher Islamic Studies.

Yaya aka yi ki ka samu kanki a harkar siyasa?

Ni za a iya cewa gadon siyasa na yi, don babata ana ce mata Hajiya Asabe Reza, ta yi gwagwarmaya sosai a ɓangaren siyasar Atiku Abubakar. Har yanzu ma kuma akwai qanina Abubakar Sadeeq da yake cigaba da siyasa a wannan gidan, tare da Turakin Adamawa na yanzu, Muhammad Atiku Abubakar. Lokacin da na taso ni ma sai na fara nuna sha’awar shiga harkokin siyasar, amma sai na ji tsoron maigidana ba zai bar ni ba. Har sai daga baya da na samu goyon bayansa, kuma na haɗu da uwarɗaki tagari, inda Allah ya haɗa ni da ýar zaɓaɓɓen shugaba, wato Folashade Ahmed Tinubu. Kuma Alhamdulillahi ta riƙe ni amana, duk wani abu da ya shafi Gombe tana kira na a kai. Shi ma maigidana ban samu wata matsala da shi ba, ya ba ni amincewa da yardarsa ɗari bisa ɗari. Nima kuma ban yarda na yi sake da wani abu da zai tava mutuncin aurena da kimata, a matsayina na mace musulma ba. Duk inda zan je da ya shafi wajen Gombe da yarana nake zuwa, su ne ma suke taimaka wajen fahimtar wasu abubuwan.

Yaya aka yi bayan kin fito daga gidan siyasar Atiku Abubakar na PDP, sai kuma ga shi ke kin ware kina siyasar APC?

Ai siyasa ra’ayi ce, kowa akwai inda ya ga zai fi samun abin da yake so. Duk da yake ina ɗaukar Atiku Abubakar a matsayin uba a gare ni, saboda yadda ya riqe mahaifiyata. Amma ni tun shigowar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari cikin harkokin siyasa na ji ina sonsa. Ina son salon siyasar Buhari na kishin cigaban qasa da kare haqqin talaka. Kuma har yanzu ni Buhari shi ne madubina a siyasa, duk kuwa da maganganu da ake yi na zargin ƙuncin rayuwa a ƙarƙashin mulkinsa. Ina yin APC tun daga qasa har sama, ko a nan Gombe da ni aka yi gwagwarmayar yaƙin neman zaɓen Gwamna Muhammadu Inuwa, tun a zangon farko har zuwa na biyu, ina tare da Ko Gezau. Ýan’uwana kuma da suke PDP muna tare da su lafiya ana cigaba da zumunci.

Ga shi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana dab da sauka daga mulki, wanne abu ne za ki yi kewa game da shi?

Alhamdulillahi, abu ɗaya ne zan daɗe ina kewar tafiyar Baba Buhari, yadda yake kishin talakawa, kuma komai zai yi zai tsaya ne kan gaskiya.

Menene fatan ki ga sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da zai karvi ragamar shugabancin ƙasar nan na wasu shekaru?

Fatana shi ne sabon shugaban ƙasa mai jiran gado, idan ya zo ya yi ƙoƙari ya haɗa kan ýan ƙasa bakiɗaya a zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, babu bambancin siyasa, ko addini ko ɓangarenci. In sha Allahu ina da ƙwarin gwiwar sabon shugaban ƙasa zai zo da tsare tsaren da za su kawo wa ƙasar nan cigaba, don a samun bunƙasar masana’antu, ilimi, da samar da ayyukan yi. A kuma samu walwalar rayuwa, ýan Nijeriya su ji daɗi, su gane an samu canjin shugabanci.

Kin yi gwagwarmayar siyasa da mata daban daban, daga ciki da wajen Jihar Gombe, yaya ki ka ga ƙwazon da mata ke nunawa wajen neman haƙƙoƙinsu da ba da gudunmawa a harkokin siyasa?

Gaskiya mata sun sha gwagwar maya ba kaɗan ba, sun zage sosai sun fita an yi yaƙin neman zaɓe tare da su, sun kaɗa ƙuri’a, sun yi rawar gani. Fatana shi ne idan sabuwar gwamnati ta shigo za a tuna da wannan gagarumar gudunmawa da mata suka bayar. A bai wa masu ilimi a cikin su muqamai masu tsoka, ba muqamai na je ka na yi ka ba. A bai wa mata na birni da ƙauye jari da tallafin sana’o’in dogaro da kai.

Manazarta harkokin siyasa na ganin mata sun yi ƙaranci sosai a cikin siyasa, musamman manyan ýan boko, ba sa son shiga takara, sai dai bayan cin zaɓe a zo ana ba su kyautar kujeru, wanne jan hankali za ki yi wa mata ýan siyasa?

To, ni dai ina mai ƙara jan hankalin mata mata ýan siyasa su yi haƙuri su yi haƙuri, su riƙa fita suna takara, ana damawa da su. Su kayar, su ma a kayar da su, shi ne siyasa. A haka wata rana za a samu mace, gwamna, ko mace shugaban ƙasa, har ma da Ciyamomi da Kansiloli. Kada mu karaya, nasara daga Allah take. Na san akwai ƙalubale da yawa, da suka shafi batun iyali, addini da kuma al’ada, wanda ke razana wasu matan su gagara fitowa.

Yaya ki ka ji lokacin da aka sanar cewa Sanata Aisha Binani da ta yi takarar gwamna a Jihar Adamawa ba ta ci zaɓen ta ba?

Gaskiya ban ji dadi ba, har na yi kuka da hawaye, don ina son Sanata Aisha Binani ƙwarai da gaske, domin na ga irin ayyukan alherin da ta gudanar a Jihar Adamawa, jama’a da dama sun amfana. Mun yi baƙin ciki sosai, amma mun bar wa Allah. Ba za mu karaya ba, za mu cigaba da fita takara ana gwabzawa da mu, in sha Allah.

Yaya ki ke kallon yadda al’umma ke tsangwamar mata ýan siyasa, ke yaya ki ka fuskanci wannan matsalar?

Babu shakka akwai ƙalubale sosai, tun daga gida ma za ka ga wasu kan tunkari maigidan wata suna ce masa, yaya zai qyale matarsa tana siyasa, ko ya nuna musu ba shi da matsala da wannan, saboda ya yarda da ita, amma za ka ji wasu na ƙoƙarin nuna ai ba a yarda da mata. To, shi ya sa a duk tafiyar da zan yi ko wani wurin taron siyasa da iyalina nake tafiya. Ban tava zuwa wata harkar siyasa ni kaɗai ba, don irin yadda nake ji wasu jama’a na kallon mata ýan siyasa. Wuraren da ba zan samu damar zuwa ba, akwai sauran manyan ýan ƙungiya da nake wakiltawa su ma suna zuwa, ko kuma idan ta kama mu je tare da su.

Menene kiran ki ga sabuwar gwamnatin Jihar Gombe da za ta zo game da kula da haƙƙoƙin mata?

Ni dai fatana ga sabuwar gwamnatin da za ta zarce a zango na biyu shi ne ya ƙara ƙoƙari a kan wanda yake yi. Mun sani tun da ma gwamnan mu mai tausayin mata ne da kula da buƙatun su, Ko gezau ba ma yi kan cewa, a wannan lokacin ma da mata za a yi, don shi ma shaida ne kan irin gudunmawar da mata suka bayar wajen sake dawowar sa a karo na biyu. Muna yi masa fatan gamawa lafiya, cikin nasara da cigaba. Kuma zan yi amfani da wannan dama in taya shi murna da samun sabon shugabancin da ya yi na zama Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa, ina yi masa addu’ar Ubangiji Allah Ya ba shi lafiya da ƙwarin gwiwar ɗaukar wannan nauyi da aka ɗora masa.

Menene fatan ki na ganin kyautatawar harkokin siyasa a nan Jihar Gombe, da ma Nijeriya bakiɗaya?

Ina son siyasar cikin Gombe ta gyaru, komai ya wadata, a samu bunƙasar tattalin arziƙi da zaman lafiya. Kowa ya yi rayuwa cikin aminci da wadata.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Lallai mu tsaya mu riƙe al’adunmu da tarbiyyar mu, yadda magabatanmu suka ɗora mu a kai.

Na gode.

Ni ma na gode