10
Apr
Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na Jam'iyyar APC ya kafa kwamitin musamman mai mambobi biyar domin bincikawa da kuma sasanta tsakanin mambobin jam'iyyar. An kafa kwamitin ne domin duba batun da Shugaban jam'iyyar na ƙasa reshen Arewa maso Yamma, Salihu Moh'd Lukman, ya ɗaga a kan yadda Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakatarensa Sanata Iyiola Omisore ke gudanar da harkokin jam'iyyar. Binciken Blueprint Manhaja ya gano kwamitin da aka kafa na ƙunshe da mambobi da suka haɗa da Abubakar Kyari a matsayin Shugaba da Emma Eneukwu da Ijeomah Arodiogbu da kumaFelix Morka. Majiya mai tushe ta ce…
