02
Jun
Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta tabbatar da sako dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris. Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na hukumar, Mr Wilson Uwujaren ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ranar Alhamis a Abuja. Jami'in ya ce an ba da belin Idris ne bayan da ya cika dukkan sharuɗɗan belin da aka gidanya masa. Idan za a iya tunawa, EFCC ta cafke Idris ne ranar 16 ga Mayu bisa zargin yin sama-da-faɗi da Naira biliyan 80 mallakar gwamanti. Bayanan EFCC sun nuna Idris ya yi amfani da hanyoyi daba-daban waje…
