28
Feb
Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a jihar Adamawa sun kama wata budurwa 'yar shekara 18 mai suna Blessing John, a daidai lokacin da ta yi yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da ta sato. Da take yi wa 'yan sanda bayani, Blessing ta amsa cewa ta ƙwamuso yaron ne a Michila da nufin kai shi Mubi ta sayar don ta samu kuɗin sayen gida da mota. Blessing 'yar Unguwan Cashew da ke hanyar Babban Asibitin Michika ce. Bayanan 'yan sanda sun nuna Blessing ta yaudari yaron ne ta ɗauke shi daga Michika zuwa Anguwan Kara da ke Mubi…
