Labarai

Gwamna Bala tagomashi ne daga Allah, cewar sarakunan yammacin Afrika

Gwamna Bala tagomashi ne daga Allah, cewar sarakunan yammacin Afrika

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Babban Sakataren Ƙungiyar Ma’abuta Sarauta ta Yammacin Afirka (Association of West African Monarchs) ‘AWAM’, Kwamred Eliot Afiyo ya bayyana yaƙinin ƙungiyar na cewa Nijeriya za ta kasance kan turba ta ɗaukaka a shekara ta 2023, matuƙar Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kama ragamar shugabancin ta. Afiyo ya yi wannan furuci ne a birnin Akara ta Ƙasar Ghana a kwanakin baya yayin da yake tofa albarkacin bakin sa a wani taro na ma’abuta mulki da aka gudanar a can ƙasar. Ya ce, “Masu alfarma, girma, zatuka da abokai. Wata girmamawa ce da aka gayyace…
Read More
Azumin Ramadan: Cibiyar Saudiyya za ta ciyar da ’yan Nijeriya 12,600

Azumin Ramadan: Cibiyar Saudiyya za ta ciyar da ’yan Nijeriya 12,600

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Cibiyar Agaji ta Sarki Salman da ke ƙasar Saudi Arabiyya (KSrelief, Abibakr As-Sidiq Philanthropic Home) ta bayyana cewar, za ta ciyar da ‘yan Nijeriya da abinci a wannan wata na Sharu Ramadana da ɗaukacin Musulmin duniya suke jiran isowar sa. Shirin tallafin na Sarki Salman ‘KSrelief’ a ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairu, 2022 ne ya sanya hannu da Cibiyar Taimako da Agaji ta Ƙasar Saudiyya domin ya raba kwandunan abinci wa magidanta guda 2,300 a Nijeriya, a cikin watan Ramadan mai gabatowa. Shirin na agajin zai ciyar da Musulmi ‘yan Nijeriya kimanin dubu 12,…
Read More
Kotu ta rufe asusun ajiyar ƙananan hukumomin Katsina

Kotu ta rufe asusun ajiyar ƙananan hukumomin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta rufe asusun bankin ajiyar haɗaka ƙananan hukumomin jihar Katsina sakamakon ƙin bin umarninta da gwamnatin jihar ta yi, inda tun farko kotun ta umarci gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari akan ta biya shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da gwamnatin ta rushe a shekara ta 2015. Shugaban jam'iyyar adawa a jihar ta PDP wato Hon. Yusuf Salisu Majigiri ne ya bayyana hakan a sakatariyar jami'iyyar da ke birnin Katsina a lokacin da yake yi wa ɗaruruwan magoya bayan jam'iyyar da 'yan takarar shugabannin…
Read More
Kotu ta ba da umarnin a saki matar wanda ya kashe Hanifa

Kotu ta ba da umarnin a saki matar wanda ya kashe Hanifa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata babbar kotu da ke zamanta a Kano ta ba da umarnin a saki matar wanda ake zargi da kashe wata ’yar shekara 5, Hanifa Abubakar, da kuma binne ta a harabar makarantar da ya ke shugabanci. Matar, wacce aka zarga da haɗa baki da mijinta wajen yin garkuwa da kuma kashe ƙaramar yarinyar, an sako ta ne a ranar Juma’a. Jamila dai ta bayyana cewa, ba ta da wani laifi a lokacin da ta gabatar da shaida kan mijinta a wata babbar kotun Kano a ranar Alhamis. Tun da farko lauyan gwamnati Barista Lamido Soron…
Read More
Rundunar ‘yan sanda ta amince jami’anta mata su sanya hijabi

Rundunar ‘yan sanda ta amince jami’anta mata su sanya hijabi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, IGP Usman Alƙali Baba ya amince jami'an 'yan sanda mata Musulmi su fara sanya ɗan ƙaramin hijabi kan kayan sarki idan suna da sha'awar hakan kamar yadda sanarwar ta ce. Sanarwar ta ce an amince jami'an 'yan sandan mata su saka ƙaramin hijabi a cikin kakin da yin amfani da jakar hannu wadda hukumar ta amince da ita da kuma takalmin 'yan sanda da shi ma aka yarje musu su yi amfani da shi. Wanna shi ne karo na farko da jami'an 'yan sanda mata suka samu wannan 'yancin…
Read More
Nijeriya za ta kashe Naira biliyan uku wajen kwaso ’yan ƙasar daga Ukraine

Nijeriya za ta kashe Naira biliyan uku wajen kwaso ’yan ƙasar daga Ukraine

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da kashe Dala miliyan takwas da rabi, wato fiye da Naira biliyan uku kenan, wajen aikin kwaso 'yan Nijeriya daga ƙasashe huɗu maƙotan Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi a can. Ma'aikatar harkokin waje da haɗin gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwashe 'yan ƙasar kusan 5,000 daga ƙasashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary. Ƙaramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya faɗa wa manema labarai a ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa, cewa za a tura jirage uku don gudanar…
Read More
Za mu sasanta da Sarkin Kano, don mutum ne mai dattaku – Air Peace

Za mu sasanta da Sarkin Kano, don mutum ne mai dattaku – Air Peace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban kamfanin jirgin sama na Air Peace, Allen Onyema ya bayyana cewa hukumomin kamfanin za su ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da daɗewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru. A makon da ya gabata ne aka ɗan samu rashin jituwa tsakanin Fadar Sarkin Kano da Kamfanin na Air Peace a yayin dawowar sarkin zuwa Kano da ga tafiyar da ya yi zuwa wasu ƙasashe na Afirka. Sai dai kuma Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada ƙura ba saboda ya san Sarkin Kano mutum ne…
Read More
Za mu soma fitar da fetur ba dare ba rana – NNPC

Za mu soma fitar da fetur ba dare ba rana – NNPC

Daga BASHIR ISAH Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya ce babu buƙatar 'yan Nijeriya su riƙa sayen fetur suna ɓoyewa saboda a cewarsa an tanadi wadataccen mai da za a fitar. Shugaban NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Laraba a Abuja jim kaɗan bayan ganawarsa da ƙungiyar ma'aikatan man fetur da ƙungiyar direbobi masu jigilar mai (PTD) da ƙungiyar 'yan kasuwar mai (DAPMAN) da kuma ƙungiyar manyan 'yan kasuwar mai (MOMAN). Kyari ya ce, "ba a fama da ƙarancin mai a ƙasar nan, jerin gwanon abubuwan hawa da ake gani a gidajen mai wahala ce…
Read More
Nijeriya ta yi zargin jami’an tsaron Ukraine na hana ‘yan Nijeriya ficewa daga ƙasar zuwa Poland

Nijeriya ta yi zargin jami’an tsaron Ukraine na hana ‘yan Nijeriya ficewa daga ƙasar zuwa Poland

Daga BASHIR ISAH Yayin da ake shirin tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Ukraine, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce 'yan Nijeriya kimanin mutum dubu huɗu haɗe da wasu 'yan Afrika da dama ne suka maƙale a Ukraine. Sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu a ranar 27 ga Fabrairu ta ce, "Abu ne mai daɗaɗɗen tarihi yadda 'yan Nijeriya da sauran 'yan Africa ke tafiya karatu a ƙasar Ukraine, musmaman ma don nazarin likitanci. Kuma galibin ɗaliban 'yan jami'a ne." Garba Shehu ya ci gaba da cewa wani sahihin hoton bidiyon da gwmanati…
Read More
‘Yan bindiga sun sace amarya ana tsaka da biki a Neja

‘Yan bindiga sun sace amarya ana tsaka da biki a Neja

Daga BASHIR ISAH A ranar Asabar da ta gabata 'yan bindiga suka kai hari a ƙauyen Gbacitagi da kewaye a yankin ƙaramar hukumar Lavun a jihar Neja inda suka ɗauke amarya ana tsaka da bikin aure tare da halaka aƙalla mutum goma. Rahotanni daga yankin sun ce 'yan bindigar sun wawushe kayayyaki da kuɗaɗen da suka tarar a wajen bikin. Maharan wanda aka ce adadinsu ya haura mutum 100 sun farmaki ƙauyukan yankin ne ɗauke da muggan makamai kuma a kan babura. Haka nan, an ce 'yan bidingar sun kwashi shanu da kayan abinci masu yawan gaske yayin harin. Sauran…
Read More