Labarai

Me ya kai Aisha Buhari zauren Majalisar Dattawa?

Me ya kai Aisha Buhari zauren Majalisar Dattawa?

Daga BASHIR ISAH Bayanan da suka riski MANHAJA a daidai wannan lokaci na nuni da cewa a karon farko, uwargidan Shugaban Ƙasa Buhari, Aisha Buhari ta ziyarci zauren Majalisar Dattawa. Ziyarar Aisha ya zuwa zauren Majlisar a yau abu ne mai cike da tarihi, kasancewar wannan shi ne karon farko da irin hakan ya taɓa aukuwa a tarihin Nijeriya inda Majalisar Dattawa ta karɓi baƙuncin matar Shugaban Ƙasa. Aisha ta halarci majalisar ne don ta shaida miƙa rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan yi wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima. Majalisar ta jinkirta karɓar rahoton ne musamman don bai wa Aisha damar…
Read More
Ma’aikatar Kuɗi ta ƙaryata tashin gobara a babban ofishinta na Abuja

Ma’aikatar Kuɗi ta ƙaryata tashin gobara a babban ofishinta na Abuja

Daga BASHIR ISAH Babban Ofishin Ma'aikatar Kuɗi na Ƙasa da ke Abuja, ya ƙaryata labarin da wasu kafofin yaɗa labarai suka yayata da safiyar Larab cewa gobara ta kama ofishin. Taƙaitaccen bayanin da ma'aikatar kuɗin ta wallafa a shafinta na facebook da safen nan mai ɗauke da sa hannun mai bai wa Ministar Kuɗi shawara kan harkokin labarai da sadarwa, Yunusa Tanko Abdullahi, ya nuna abin da ya faru ba gobara ba ce, ɗan akasi ne aka samu a ma'ajin batura wanda kuma tuni an shawo kan matsalar ba tare da wani jinkiri ba. Ma'ajin batura inda akasin ya auku…
Read More
Ma’aikata ta nesanta kanta daga sanarwar bogi

Ma’aikata ta nesanta kanta daga sanarwar bogi

Daga BASHIR ISAH Ma'aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta nesanta kanta daga wata sanar da ke nuni da 'yan ƙasa su dakatar da tafiye-tafiye zuwa wasu keɓaɓɓun ƙasashen waje har zuwa ƙarshen watan Mayun 2022. Cikin sanarwar manema labarai da Ma'aikatar ta fitar a jiya Talata, ta ce sanarwar dakatar da tafiye-tafiyen ba gaskiya ba ne kuma ba daga gare ta take ba. An ga wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 18/02/2022 da aka yaɗa mai nuni da hana 'yan Nijeriya tafiye-tafiye zuwa ƙasashen da suka haɗa da; Belarus, Poland, Slovakia, Hungary, Romania da kuma Moldova wai har sai…
Read More
Kotu za ta tsare Abba Kyari na tsawon kwanaki 14

Kotu za ta tsare Abba Kyari na tsawon kwanaki 14

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau Talata ne babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayyana tsare Abba Kyari da wani mai taimaka masa na tsawon kwanaki 14, bayan da ta amince da buƙatar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), na neman izinin ci gaba da tsare mataimakin kwamishinan ’yan sandan da aka dakatar, DCP, Abba Kyari da wasu mutane shida, na tsawon kwanaki 14. Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, ta shaida wa kotun cewa, waɗanda ta nemi a ci gaba da tsare su a hannunta, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 4 a Neja

‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 4 a Neja

Daga BASHIR ISAH Wasu 'yan bindiga sun halaka jami'an 'Civil Deffence' huɗu tare da ƙona wasu mutanen da ba tantance adadinsu ba ƙurmus a ƙauyen Galadiman Kogo da ke yankin ƙaramar hukumar Shiroro a Jihar Neja. Shaidu sun ce haka waɗannan mutanen da aka cinna ma wuta suka ƙone ƙurmus ba tare da samun agaji ta kowane ɓangare ba, don kuwa duk wanda ya leƙo waje a wannan lokacin 'yan bindigar za su harbe shi. Kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Mr Monday Kuryas ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce jami'an tsaron NSCDC su huɗu tare…
Read More
‘Yan sanda sun ceto mata bakwai da kashe ɗan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun ceto mata bakwai da kashe ɗan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga tare da ƙwato mata 4 da ƙananan yaransu guda 3 a ƙauyen Gandun Ƙarfi dake cikin ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina. Kakakin rundunar  SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan jiya alhamis 17 ga Fabarairu, 2022 a wani taron manema labarai da rundunar ta kira don sanar da al'umma yadda jami'an 'yan sanda ke ƙoƙarin yaƙar 'yan ta'adda da suka addabi wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar. SP Isa ya bayyana cewar 'yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun afkawa ƙauyen Gandun…
Read More
Saraki ya yi jawabi a taron masu gidajen rediyo da talabijin na Arewa

Saraki ya yi jawabi a taron masu gidajen rediyo da talabijin na Arewa

Daga WAKILINMU Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya gabatar da jawabi a taron shekara na masu gidajen talabijin da rediyo na arewacin Nijeriya. Saraki ya yi jawabi ne jiya Litinin, mai taken 'SHAN MIYAGUN ƘWAYOYI A AREWA, DA RAWAR DA KAFAFEN WATSA LABARAI ZA SU TAKA WURIN DAƘILE ANNOBAR' a wurin taron kungiyar ta NBMOA a ɗakin taro na otal ɗin Bristol dake Birnin Kano. Bukola Saraki wanda ya samu wakilcin tsohon kakakin majalisar jihar Kwara, Hon. Ali Ahmed ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai da su tashi tsaye wurin kawo…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta yi alƙawarin kyautata rayuwar waɗanda ba ’yan asalin jihar ba

Gwamnatin Zamfara ta yi alƙawarin kyautata rayuwar waɗanda ba ’yan asalin jihar ba

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin jihar Zamfara ta yi alƙawarin ci gaba da samar da yanayi mai kyau wajen ganin ta inganta rayuwar waɗanda ba ‘yan asalin jihar dake zaune a jihar domin su zauna lafiya da al’ummar da suke zaune. Sabon mai bai wa Gwamna Bello Matawallen Maradun shawara na musamman Hon. Aliyu Ɗansadau ya bayyana haka a lokacin da ya karvi baƙuncin ƙungiyar waɗanda ba ‘yan asalin jihar ba da suka raka shi don kama aiki a ofishin sa. Ɗansadau ya bayyana irin gudunmawar da al’ummar da ba ’yan asalin jihar suke bayarwa ta fuskar siyasa da…
Read More
DCP Abba Kyari ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu

DCP Abba Kyari ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu

Daga BASHIR ISAH DCP Abba Kyari wanda yake tsare a hannun hukumar NDLEA bisa zargin fataucin miyagun ƙwayoyi, ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu a ranar Litinin. Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, cikin ƙararsa da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, Kyari ya buƙaci kotu da ta talista wa Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) kan ta bada belin shi saboda dalilai na kula da lafiyarsa kafin lokacin da za a saurari shari'arsu. Cikin takardar da ya tura wa kotu ta hannun lauyarsa, Mrs. P. O. Ikenna, Kayari ya shaida wa kotu cewa ana tsare da shi ne…
Read More
Ɗan jarida, Dahiru Muhammad ya zama Kachallan Kutumbawa

Ɗan jarida, Dahiru Muhammad ya zama Kachallan Kutumbawa

Daga WKAILINMU Dakacin Kutumbawa a jihar Kano, Alhaji Mustapha Abubakar Rimin Kira ya amince da a naɗa ɗan jarida Dahiru Muhammad Maihula a matsayin Kachallan Kutumbawa. Cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Dakacin Kutumbawa ya ce kwamitin naɗin ya amince da naɗin Dahiru Maihula ne duba da cewa shi hazaƙin mutum ne. Yanzu haka Dahiru Maihula Darakta ne a wani kamfanin yaɗa labarai da ke Kano, wato DMM. Sarakunan da Kano ta yi daga zuri'ar Kutumbawa sun haɗa da:(1) Muhammadu Alwali Kutumbi.1623-1643(2) Alhaji Dan Kutumbi.1648-1649(3) Shekarau (ll) 1649-1651(4) Muhammadu Kukuna.1651-1652(5) Sarki Soyaki.yayi sarki sau biyu,1652(6) Sarki Bawa. 1660-1670(7)…
Read More