23
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Darakta Janar na Ƙungiyar Gwamnonin APC, Mohammed Salihu Lukman, ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga ƙungiyar ta PGF. Murabus ɗin nasa a ranar Litinin ya zo ne sa’o’i 24 bayan ganawar gwamnonin jam’iyyar APC a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi a daren Lahadi, a daidai lokacin da APC ke cikin tsaka-mai-wuya na rashin tantance ranar da za ta zaɓi sabbin shuwagabannin ta. Manhaja ta ruwaito a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Lukman ya ce ya guje wa yin tsokaci ne kan murabus ɗin nasa saboda jam'iyyar ba ta riga ta amince da…
