Labarai

HOTUNA: Ziyarar Osinbajo a Kano

HOTUNA: Ziyarar Osinbajo a Kano

A Talatar da ta gabata Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Kano. Osinbajo ya ziyarci Kano ne don halartar taron Lakcar Tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardauna wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta saba shiryawa duk shekara.
Read More
Allah Ya yi wa ɗan uwan Gwamna Tambuwal, Muhammadu Bello rasuwa

Allah Ya yi wa ɗan uwan Gwamna Tambuwal, Muhammadu Bello rasuwa

A yammacin jiya Talata Allah Ya yi Muhammadu Bello (Wazirin Tambuwal) rasuwa. Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun ƙanin marigayin kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, CFR, (Mutawallen Sakkwato). Sanarwar ta nuna Marigayin ya shafe shekaru 37 riƙe da muƙamin Wazirin Tambuwal tun bayan da ya gaji mahaifinsu, Alhaji Umar Waziri Usmanu. Kazalika, sanarwar ta ce da safiyar Larabar nan za a yi janai'zar marigayin. Gwamna Tambuwal A ƙarshe, Mutawallen Sakkwato ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, kana Ya sanya Aljannar Firdausi ita ce makomarsa.
Read More
Shaidar kammala sakandare ta yi kaɗan ga batun tsayawa takara – Gbajabiamila

Shaidar kammala sakandare ta yi kaɗan ga batun tsayawa takara – Gbajabiamila

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa duba da zamani yau, mallakar shaidar kammala makarantar sakandare ko makamancin haka a matsayin mafi ƙarancin zurfin karatu bai wadatar ba ga duk wani mai sha'awar riƙe muƙamin gwamnati. Don haka ya yi kira da a yi wa Sashe na 131 (d) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima domin ɗaga mafi ƙarancin shaidar kartun da ya zama wajibi a mallaka kafin tsayawa takarar neman muƙaman gwamnati. A cewar Gbajabiamila, tanadin shaidar karatu mafi ƙarancin da kundin tsarin mulkin ke nunawa a yanzu abu ne…
Read More
Dokar Zaɓe: Kada ku ɗauki matsayar Buhari da rashin muhimmaci, gargaɗin Jega ga ‘yan Majalisun Tarayya

Dokar Zaɓe: Kada ku ɗauki matsayar Buhari da rashin muhimmaci, gargaɗin Jega ga ‘yan Majalisun Tarayya

Daga BASHIR ISAH Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Attahiru Jega, ya faɗa wa Majalisar Tarayya cewa ɗaukar matsayar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari game da batun yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima da rashin muhimmanci ba ita ce hanya mai ɓulewa ba ga ƙasar nan. Jega ya yi wannan furici ne a wajen wani taro kan Dokar Zaɓe ta 2021 wanda cibiyar Yiaga Africa tare da abokan hulɗarta suka shirya ranar Lahadi a Abuja. A cewar Jega, lamarin zai fi yi wa ƙasa armashi idan ta shiga sha'anin zaɓe na gaba da sabuwar dokar zaɓe, yana mai cew hakan zai…
Read More
Sabon rikicin al’ummar Filato ya laƙume rayukan mutane 18

Sabon rikicin al’ummar Filato ya laƙume rayukan mutane 18

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Shugaban Ƙungiyar cigaba na ƙasa na al’ummar Irigwe a Jihar Filato ya gano waɗanda aka yi wa kisan gilla a daren Talata da ta gabata a ƙauyen Ancha ta masarautar Irigwe cikin ƙaramar hukumar Bassa na jihar. Ƙungiyar ta bayyana cewar, mutane 18 ne suka rasa rayukan su a cikin farmakin na Irigwe da ya ɗauki tsawon lokaci na fiye da awowi biyu ana tabka shi. Da yake bayar da ba’asin ƙididdiga akan farmakin, Sakataren ƙasa na ƙungiyar cigaban ta Irigwe, tare da wasu jami’an ƙungiyar, Davidson Malison, ya ce “yayin da wasu jama’a…
Read More
Mun sasanta ma’aurata 3,579 a Jigawa – Hisbah

Mun sasanta ma’aurata 3,579 a Jigawa – Hisbah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta sasanta ma'aurata 3,579 a 2021, kamar yadda Kwamnadan ta na jihar, Ibrahim Ɗahiru ya bayyana. Ɗahiru ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN, a Dutse a Alhamis da ta gabata. Kwamnadan ya yi bayanin cewa haƙƙin hukumar ne ta sasanta ma'aurata.Ya kuma bayyana cewa hukumar ta sasanta tsakanin 'yan kasuwa 41, iyaye da 'ya'yn su 221, maƙwabta 319 da manoma da makiyaya 71. "Sasanta tsakanin al'umma abu ne mai amfani da ya ke wanzar da soyayya da zaman…
Read More
Hukumar ‘Civil Defence’ ta haramta ayukkan jami’anta na sa-kai a Sakkwato

Hukumar ‘Civil Defence’ ta haramta ayukkan jami’anta na sa-kai a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Hukumar samar da tsaro ga farin kaya ta Civil Defence ta haramta ayukkan jami'anta na sakai a Sakkwato wato boluntiya da ke aiki ƙarƙashin hukumar. Ɗaukar wannan matakin da hukumar ta yi dai ya biyo bayan yawaitar zarge-zargen aikata ababen da suka saɓa wa doka daga jami’an hukumar na sa kai. A wata sanarwa da hukumar ta fitar wadda ke ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar da ke Jihar Sakkwato, Hamza Adamu Illela, hukumar ta bayyana cewa izuwa yanzu ta dakatar da dukkan ayyukkan waɗannan jami'an sa kai saboda samun su…
Read More
Sai Gwamnatin Buhari ta sauka ‘yan Nijeriya za su riƙa yaba ayyukanmu – Sanata Lawan

Sai Gwamnatin Buhari ta sauka ‘yan Nijeriya za su riƙa yaba ayyukanmu – Sanata Lawan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana cewa, mafi yawan ’yan Nijeriya na kwana da tashi cikin farin ciki da su ’yan majalisa. Wannan farin cikin kuwa, jin daɗi ne da su ke yi ga mulkin Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce, sai ma bayan sun kammala wa’adin mulkinsu ne akasarin ‘yan Nijeriya za su riƙa santin rubutawa da furta kalaman alheri kan Majalisar Dattawa da ta Wakilai da ma Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, dangane da ɗimbin nasarorin da suka samar. Lawan ya yi wannan bayani ne a wurin wani taron taya shi…
Read More
Shan ƙwayoyi da karuwanci suka jawo rufe sansanin ’yan gudun hijira a Maiduguri – Zulum

Shan ƙwayoyi da karuwanci suka jawo rufe sansanin ’yan gudun hijira a Maiduguri – Zulum

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri  Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rufe sansanonin 'yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri, inda ya ƙara da cewa saboda yadda aka wayi gari baɗalar karuwanci, shan miyagun ƙwayoyi, da makamantan su ne ke neman mamaye matsugunan.  Har wala yau, gwamnan ya ƙara da cewa, babu wani shugaba mai kishin al'ummar sa da zai zuba ido hakan ta ci gaba da faruwa ga jama'ar da ya ke shugabanta. Gwamna Babagana Zulum ya bayyana hakan a jawabin murna da sabuwar shekara wanda ya yi…
Read More