29
Oct
Daga NASIR S. GWANGWAZO Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙulla yarjejeniya da rundunar sojin ƙasar Najeriya domin magance matsalolin tsaro a faɗin ƙasar haɗa da yankin sahel. Babban Wakilin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Africa ta Tsakiya, Mai girma Mahamat Khatir Annadif, shi ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar sa ga Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya a Shelkwatar rundunar da ke Abuja. Inda yaba wa rundunar sojin Nijeriya kan sha'anin magance matsalolin tsaro ƙasar da kuma yankin sahel. Jakadan ya na tare ne da Wakilin Musamman na Babban Sakataren Majalisar, Mai girma Mr Francois…
