Labarai

Tsohon gwamnan Ekiti, Fayose ya ɗare acaɓa a Legas

Tsohon gwamnan Ekiti, Fayose ya ɗare acaɓa a Legas

A wani mataki don gudun kada jirgin sama ya baro shi a tasha, ya sanya tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, ya hau acaɓa zuwa babban filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Wani hoton gwamnan da ya karaɗe kafafen sadarwa, ya nuna yadda tsohon gwamnan tare da dogarinsa suka hau acaɓa guda don a kai su filin jirgin. Tsohon gwamnan shi da kansa ya soma yaɗa hoton a shafinsa na facebook inda ya nuna matsalar cunkoson abubuwan hawa a Legas babu ruwanta da ko kai waye, wanda ala tilas ya zaɓi hawa acaɓa son jada ya rasa…
Read More
Sojoji sun gasa wa mayaƙan Boko Haram/ISWAP gyaɗa a hannu a Wulgo

Sojoji sun gasa wa mayaƙan Boko Haram/ISWAP gyaɗa a hannu a Wulgo

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga babban ofishin sojojin Nijeriya da ke Abuja, na nuni da cewa sojojin rundunar 'Operation Haɗin Kai' da ke aikin haɗin gwiwa da sojojin Kamaru a yankin Arewa-maso-gabas, sun kakkaɓe wasu mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin Wulgo. Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na facebook mai ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama'a na Rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, rundunar ta ce a ranar Litinin da ta gabata sojojin suka samu wannan nasarar a kan 'yan ta'addan inda suka yi fatafata da su. Sanarwar ta ce 'yan bindigar sun cimma…
Read More
Hukumar EFCC ba ta cafke ni ba- Sanata Kwankwaso

Hukumar EFCC ba ta cafke ni ba- Sanata Kwankwaso

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Tsohon gwamna jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa ta EFCC ta cafke shi. Hakan na cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Sanata Kwankwaso ya fitar a yau Lahadi. Ta cikin sanarwar dai, Kwankwaso ya ce, shi da kansa ne ya je ofishin hukumar domin wanke kansa dangane da wasu zarge-zarge marasa tushe da ake yi masa. Kazalika ya ƙara da cewa, “Na ziyarci shalkwatar hukumar jiya Asabar domin bata bayanai, kuma…
Read More
Sojoji sun musunta jita-jitar Injiniyoyinsu na gina ruga a Inugu

Sojoji sun musunta jita-jitar Injiniyoyinsu na gina ruga a Inugu

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Larabar da ta gabata ne, Rundunar sojojin tawaga ta 82 suka ƙaryata wani labari da yake ta zazzagawa a kan cewa Sojojin Nijeriya suna gina gidajen makiyaya wato ruga a cikin garruwan Ochima da Affa da ke ƙananan hukumomin Igbo-Etiti da Udi dukkansu a jihar  Enugu. Tawagar sojojin ta ambaci labarin da labarin ƙanzon kurege, kuma maras tushe balle makama. Wannan bayani dai yana ƙunshe ne a cikin wata takarda da rundunar ta wallafa, wacce mataimakin riƙo ga jami'in hulɗa da jama'a na sojojin Najeriya wato Manjo Abubakar Abdullahi ya sanya wa hannu. Abdullahi…
Read More
2023: Katinka shi ne makaminka, cewar Sa’adu Gulma

2023: Katinka shi ne makaminka, cewar Sa’adu Gulma

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Shugaban Jam'iyyar APC Arewa na jihar Legas, Alhaji Sa'adu Yusuf Dandare Gulma ya yi kira ga ’ya’yan jam'iyyar APC musamman ’yan Arewa mazauna kudancin ƙasar nan da su tabbatar da kowa ya yi rajista ta jam'iyya da kuma jifa ƙuri'a. Ya yi wannan kiran ne ranar Laraba da ta gabata a ofishinsa inda ya karɓi baƙuncin shugabannin gamayyar ƙungiyoyin matasan jihohi goma sha tara na arewacin ƙasar nan. Alhaji Sa'adu Gulma ya ce, yin rajista ga ɗan siyasa wajibi ne saboda duk yadda ka ke son mutum idan ranar zaɓe ta zo ba ka…
Read More
Sojoji sun yi artabu da tserarrun ‘yan bindigar Zamfara a Neja

Sojoji sun yi artabu da tserarrun ‘yan bindigar Zamfara a Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Jami'an tsaron haɗin gwiwa na Nijeriya sun kasha aƙalla 'yan bindiga 32 da suka tsere daga Zamfara a jihar Neja. Hakan ya faru ne bayan da 'yan bindigar suka kai hari kan ofishin tsaro, suka harbe 'yan sanda biyar da suka yi ƙoƙarin fuskantar su. Lamarin ya faru ne a Bangu Gari da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar. Wata majiyar tsaro ta shaida wa manema labarai cewa, 'yan bindigar da suka tsere daga jihar Zamfara saboda ayyukan da sojoji ke yi, da farko sun yi ɓarna a cikin al'umma. Majiyar ta ƙara da…
Read More
Rundunar sojoji sun tabbatar da mutuwar Shugaban mayaƙan ISWAP, Al-Barnawi

Rundunar sojoji sun tabbatar da mutuwar Shugaban mayaƙan ISWAP, Al-Barnawi

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Kwamandan rundunar sojojin Najeriya ya bayyana cewa, Jami'an Sojin Najeriya sun kashe Shugaban ƙungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP, wato Abu Musab Al-Barnawi. Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban Jami'an tsaro, Janar Lucky Irabor. Wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ranar alhamis ɗin da ta gabata a A birnin tarayyar Abuja. Kodayake, Janar Irabo bai bayyana ainahin cikakken bayani a kan yadda jami'an suka aike da shugaban 'yan ta'addan barzahu ba. Amma ya ce: " zan iya ba ku tabbacin cewa Al-barnawi dai tasa ta ƙare, kuma ya mutu shikenan." Shi dai Al-Barnawi,…
Read More
Ɗaliban kwalejin Yawuri sun shaƙi iskar ‘yanci bayan kwana 118

Ɗaliban kwalejin Yawuri sun shaƙi iskar ‘yanci bayan kwana 118

Daga NASIR S. GWANGWAZO Kimanin ɗalibai da ma'aikata sama da 90 da aka sace a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yawuri a Jihar Kebbi sun shaƙi iskar 'yanci bayan kwanaki 118. Rahotanni daga jihar sun bayyana cewa, mahaifin ɗaya daga cikin ɗaliban da aka kama, wanda bai so a ambaci sunansa, shine ya tabbatarwa da Daily Trust hakan a daren nan, kamar yadda jaridar ta wallafa a shafinta. Ƙarin bayani na nan tafe…
Read More
Khadi Inuwa Aminu ya zama Wazirin Zazzau

Khadi Inuwa Aminu ya zama Wazirin Zazzau

Daga BASHIR ISAH Masrautar Zazzau a jihar Kaduna ta naɗa Khadi Muhammad Inuwa Aminu a matsayin Wazirin Zazzau. Masarautar Zazzau ta tabbatar da naɗin Aminu a matsayin Waziri ne cikin wasiƙar da ta aika masa mai ɗauke da sa hannun Sakataren masarautar, Alhaji Barau Musa (Sarkin Fulanin Zazzau). Sakataren ya bayyana cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Oktoba, 2021 cewa, "Bayan gaisuwa mai yawa. An umurce ni da in sanar da kai cewa, bisa umurnin Gwamnatin Jhar Kaduna ta ranar 20/09/2021 a takardarta mai lamba GHIKD/ 578, Maimartaba Sarkin Zazzau ya tabbatar maka da Sarautar Wazirin Zazzau,…
Read More