12
Oct
Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sauya wasu kwamishinoni da wasu manyan jami’an gwamnati a ƙoƙarin da yake yi na kawo sababbin jini a gwamnatinsa. Sanarwar da ta fito daga Fadar Gwamnatin jihar wadda ta sami sa hannun Mai Ba Gwamna Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Muyiwa Adekeye, ta bayyana cikin kwamishinoni 14, an canza wa kwamishinoni takwas ma’aikatu. Kwamishinonin da ba a taɓa ba sun haɗa da: Kwamishinan Kuɗi, Kwamishinan Shari’a, Kwamishinan Gidaje da Raya Birane, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida da kuma Kwamishinan Jin Daɗi da Walwalar Al’umma. Sanarwar ta ƙara da cewa, Muhammad…
