07
Oct
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ƙarƙashin Alƙali Abang Okon, ta yanke wa ɗan gidan Abdulrashid Maina, wato Faisal hukuncin ɗauri na shekara 14 a gidan yari. Tare kuma da umurtarsa da ya maido da kuɗi Naira miliyan 58 da dubu 100 ga Gwamnatin Tarayya. A wannan Alhamis ɗin Kotun ta yanke wannan hukuncin, inda ta tuhumi Faisal Maina da laifuka uku da suka haɗa da almundahana da safarar kuɗi ba bisa ƙa'ida ba, kuma an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar ne a kan ko wane laifi. Lauyan gwamnati da ke wakiltar hukumar EFCC da ta shigar da…
