30
Sep
Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin Ma'aikatar Agaji, Jinƙai da Kyautata Rayuwar 'Yan Ƙasa, ta ƙaddamar da shiri na musamman kan yaƙi da yunwa mai taken 'Project Zero Hunger' a ƙaramar hukumar Keffi, jihar Nasarawa. Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a ƙofar fadar masarautar Keffi a ranar Alhamis, tare da raba kayayyakin masarufi ga mutum sama da ɗari, maza da mata. Kayayyakin da aka raba sun haɗa da;shinkafa, wake man girki, magi, tocila, omo, atampa, sabulai da sauransu, wanda aka kimtsa su cikin wani akwatin roba na musamman. Da yake jawabi a madadin Hon. Kwamishina Iman Sulaiman Ibrahim wadda…
