Labarai

Ganduje ya naɗa sabon Sarki a Gaya

Ganduje ya naɗa sabon Sarki a Gaya

Daga AMINA YUSUF ALI A daren Asabar ɗin da ta gabata ne, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin sabon Sarkin Gaya. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da naɗin a cikin wata sanarwar da safiyar ranar Lahadi. Shi dai wannan sabon sarki, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ana ganin ya tsallake rijiya da baya ne, bayan ya ka da kusan fiye da mutane 40 waɗanda aka ce su ma suna zawarcin wannan kujera. Kuma kafin naɗin sa, sabon Sarkin, wanda ɗa ne ga marigayi Sarki Ibrahim Abdulkadir, kirmau…
Read More
EFCC ta kama bokan da ya wanki majinyancin attajiri miliyan N16

EFCC ta kama bokan da ya wanki majinyancin attajiri miliyan N16

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu haka dai wani ɗan damfara wanda ya wanke wani mutum mai neman ku]i har zunzurutun Naira miliyan 16 ya fa]a komar hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC. Hukumar EFCC ɗin ta yankin garin Maiduguri ta samu nasarar damƙe wani wanda ya yi ikirarin shi boka ne, Mohammed Ibrahim, da kuma abokin aikinsa, a kan zargin wankiyar  Naira miliyan sha shida ga Mohammed Gaji. Muhammad Ibrahim da Ibrahim Abubakar ana zargin su ne da amsar waɗancan maƙudan kuɗaɗe daga Muhammad a matsayin sadaka don a…
Read More
Tsohon Sarkin Kano ya ziyarci Sarkin Musulmi

Tsohon Sarkin Kano ya ziyarci Sarkin Musulmi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Sheikh Inyass, Khalifa Sanusi Lamido Sanusi ll ya kai ziyara a fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III. Yayin ziyarar, Khalifa Sanusi ya bayyana Sarkin Musulmin cewa, shi da tawagarsa sun zo fada ne domin yin gaisuwar ban girma da kuma neman sanya albarka, da ma gabatar wa Mai Alfarma takardar da aka bai wa Mai Martaba Sarki Sanusi na Khalifancin Ɗarikar Tijjaniyyah ta Nijeriya. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Sheikh Inyass, Khalifa…
Read More
‘Yan bindiga ba su da addini, kamar dabbobin daji su ke – Masari

‘Yan bindiga ba su da addini, kamar dabbobin daji su ke – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya bayyana cewar, 'yan bindigar da ke aikace-aikacen ta'addanci a jihohin arewa maso yamma kamar dabbobin daji su ke, kuma mutane ne waɗanda ba su da addini ko alƙibla. "Aikace-aikacen 'yan bindiga a jihohin arewa maso yamma da wa su sassan Arewa ta tsakiya ya sauya zuwa aikin ta'addanci, saboda haka mun fito da dabaru daban-daban don yaƙar wannan musiba. "Waɗannan mutane ba su da aƙida ko addini ko kuma alƙibla, kamar dabbobin daji suke", inji Masari. Gwamna Masari yana magana ne a lokacin da ya karɓi…
Read More
Ko a masallacin Makka da Madina ba zan nemi gafarar Masari ba, cewar Mahdi Shehu

Ko a masallacin Makka da Madina ba zan nemi gafarar Masari ba, cewar Mahdi Shehu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kamfanin Dialogue Group, Shehu Mahdi, ya ƙaryata wasiƙar neman afuwar Gwamnan Katsina, Bello Masari, kan batun yaɗa bayanan bogi a kansa da aka ce ya aika wa gwamnan. A ranar Alhamis, 23 ga Satumban 2021 aka ga bayyanar wata wasiƙa ta neman yafiya zuwa ga Gwamna Masari da ma al'ummar jihar wadda aka ce Mahdi ne ya rubuta tare da aikawa da ita ga gwamnan. Sai dai, cikin wani saƙon bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa mai tsawon minti 10, an ga Shehu Mahdi na bayani cikin harshen Ingilishi inda ya ƙaryata wasiƙar, yana mai cewa…
Read More
Ku guji yin tazarce – Buhari ya ja kunnen shugabannin ƙasashe

Ku guji yin tazarce – Buhari ya ja kunnen shugabannin ƙasashe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya shawarci shuwagabannin ƙasashen duniya da kada su yi riƙo da madafun iko bayan wa'adin mulkin su na tsarin mulki. Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin da yake jawabi sama da shugabannin duniya 80 a wurin babban taro na 76 na Majalisar Ɗinkin Duniya a New York. Buhari ya yi kalaman ne ƙasa da shekaru biyu ga zaɓen 2023 inda ake sa ran zai miƙa mulki ga Shugaban Nijeriya na gaba bayan shekaru takwas a Aso Rock. Buhari, wanda kuma ya kasance tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja tsakanin 1983…
Read More
Hukumar Jami’ar Bayero ta yi ƙarin hutu ga ɗalibanta

Hukumar Jami’ar Bayero ta yi ƙarin hutu ga ɗalibanta

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da yin ƙarin wa’adin komawar ɗalibai zangon karatu na 2021 da 2022. Ƙarin hutun na cikin wata sanarwar da jami’in yaɗa labaran jami’ar, Lamara Garba Azare, ya fitar mai ɗauke da sa hannun maga-takardan jami’ar, Malam Jamilu Ahmad Salim. Sanarwar ta ce, an cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar zartaswar jami’ar karo na 392 da aka gudanar a Larabar da ta gabata. A baya dai jami’ar ta sanya ranar 4 ga watan Oktoban 2021 a matsayin ranar komawar ɗaliban, sai dai yanzu an mayar da komawar ɗaliban…
Read More
Jami’an tsaro sun gano gawar da aka jefa cikin masai a Haɗejia

Jami’an tsaro sun gano gawar da aka jefa cikin masai a Haɗejia

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Wani magidanci da ke garin Haɗejia mazaunin Unguwar Kwarin Manu ya sanar da jami'an tsaro dake aiki da rundunar Civil Defense cewar yana jin wari nai tsananin gaske a masan sa, lamarin da ya sa jami'an tsaron ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka garzaya gidansa domin ba shi gudunmawar da yake buƙata. Zuwan su gidan mutumin mai suna Umar Muhd mai shekara 47 ke da wuya sai suka farke masai ɗin da yake masu bayanin yana jin wancan wari marar iyaka, bu]e masan ke da wuya sai suka ci karo da gawar…
Read More
Mahdi Shehu ya nemi afuwar Gwamna Masari kan yaɗa bayanan bogi

Mahdi Shehu ya nemi afuwar Gwamna Masari kan yaɗa bayanan bogi

Daga BASHIR ISAH Shugaban kamfanin Dialogue Group, Muhammad Mahdi Shehu, ya miƙa ƙoƙon neman afuwa ga Gwamnan Katsina, Bello Masari kan cewa ya dubi Allah sannan ya yi masa afuwa dangane da bayanan ƙarya da ya ce ya yi ta yaɗawa a kan gwamnan da gwamnatinsa wanda suka taɓa mutunci da martabar gwamnan da ma gwamnatinsa. Shehu ya nemi afuwar Masari ne cikin wata wasiƙa da ya fitar mai ɗauke da kwanan wata, 23 ga Satumban 2021. Afuwar da Shehu ya nema ta haɗa har da ta al'ummar Jihar Katsina baki ɗaya bisa yadda ya yi ta yaɗa bayanan bogin…
Read More