Labarai

An dangata wasu tsoffin gwamnonin Nijeriya da dukiyar sata a Birtaniya

An dangata wasu tsoffin gwamnonin Nijeriya da dukiyar sata a Birtaniya

Daga WAKILINMU Wani sabon rahoto da aka fitar kwannan ya nuna yadda wasu tsofoffin gwamnonin Nijeriya su goma ke da alaƙa da wasu tarin haramtattun kadarori a Ƙasar Birtaniya wanda darajarsu ta kai Pan milyan £56, wato kwatankwacin Naira bilyan N30 kenan. Rahoton kan hada-hadar haramtattun kuɗaɗe (IFF) daga Nijeriya zuwa Birtaniya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ya kuma nuna wasu kadarori 216 mallakar wasu jami’an Nijeriya su 13 da aka girke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. A cewar jaridar SaharaReporters, an gabatar da rahoton ne a wajen taron da cibiyar Human and Environmental Development Agenda tare da haɗin gwiwar Gidauniyar MacArthur…
Read More
Gwamnati na aiki tuƙuru kan karɓo sauran ‘yan matan Chibok – Minista Sadiya

Gwamnati na aiki tuƙuru kan karɓo sauran ‘yan matan Chibok – Minista Sadiya

Daga AISHA ASAS Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta na ci gaba da aiki ba tare da gajiyawa ba domin ta ceto sauran 'yan matan Chibok waɗanda aka sace shekaru bakwai da su ka gabata. Ministar ta yi wannan maganar ne a ranar Laraba lokacin da ta ke jimamin abin baƙin cikin nan da ya faru na satar ɗaruruwan 'yan matan daga makarantar su ta kwana da ke garin Chibok a Jihar Borno. Mayaƙan Boko Haram ne su ka sace 'yan matan. Sadiya Farouq ta ce ta na matuƙar…
Read More
Rikicin ƙabilanci ya ci mutum biyar a kan iyakar Gombe da Adamawa

Rikicin ƙabilanci ya ci mutum biyar a kan iyakar Gombe da Adamawa

Daga AISHA ASAS Kimanin mutum biyar ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon rikicin ƙabilanci da ya auku a yankin garuruwan Nyuwar/Jessu masu maƙwabtaka da juna a kan iyakar Gombe da Adamawa inda ƙabilun Waja da Lunguda ke da zama. Wani ganau da ya shida faruwar rikicin ya bayyana cewa saɓanin ya faru ne sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin maharba daga Jessu da kuma Fulanin Lunguda a Adamawa, waɗanda tun ba yau ba babu alaƙa ta lumana a tskaninsu. Majiyar Manhaja ta ce yayin da maharban Jessu suka tafi daji farauta ne sai matasan Fulani suka tsinkaye su…
Read More
Legas: Ɗan sanda ya rasa aikinsa bayan da aka same shi da yinƙurin hallaka budurwarsa da bindiga

Legas: Ɗan sanda ya rasa aikinsa bayan da aka same shi da yinƙurin hallaka budurwarsa da bindiga

Daga UMAR M. GOMBE Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kori jami'inta Sergeant Eze Aiwansoba bayan da ta kama shi da laifin yinƙurin kisa sakamakon harbin da ya yi wa budurwarsa Joy Ndubueze a baki da bindiga. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya faɗa a wata sanarwar da ya fitar a Litinin da ta gabata cewa, baya ga korar da aka yi wa jami'in daga aiki an kuma gurfanar da shi a wata kotun majestare da ke Yaba bisa tuhumar kisa. A cewar Adejobi, “Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kori wani Sergeant Eze Aiwansoba daga…
Read More
Bauchi: Gwamna Bala ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar JAMB/UTME, NECO

Bauchi: Gwamna Bala ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai kuɗin jarrabawar JAMB/UTME, NECO

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai 3,810 da suka samu sakamako mai kyau na auna fahimtar SSCE da aka yi musu kuɗin rajistar UTME. Haka nan, gwamnan ya amince ya biya kuɗin jarrabawar NABTEB ga ɗalibai 1,751 da ke ajin ƙarshe a makarantun fasaha da ke jihar, da kuma ɗalibai 499 daga makarantun koyon Larabci da ke shirin rubuta jarrabawar NBAIS bayan su ma an auna fahimtarsu. Bugu da ƙari, gwamnan ya ɗauki nauyin biya wa ɗalibai 11,580 da suka samu sakamako mai kyau na gwajin da aka yi musu,…
Read More

Majalisa ta gayyaci tsohon shugaban FMBN kan badaƙalar kwangilar bilyan N3

Daga AISHA ASAS Majalisar Dattawa ta hannun kwamitinta mai bin diddigin ayyukan gwamnati (SPAC), ta kirayi tsohon shugaban Bankin Bada Bashi (FMBN), Malam Gimba Yau Kumo, da ya bayyana a gabanta kan badaƙalar kwangilar Naira bilyan N3 da aka bayar. Kamar yadda rahoton da aka miƙa wa Ofishin Babban Jami'in Bincike na Ƙasa ya nuna, an bayar da kwangilar ne rukuni-rukuni har huɗu wanda hakan ya yi sanadiyar biyan kuɗi wuce abin da ya kamata a biya da Naira milyan N118,717,892. Bayanan Odita Janar wanda Shugaban Kwamitin Majalisar, Sanata Mathew Urhoghide (PDP Edo ta Kudu), ya bayyana wa manema labarai…
Read More

‘Operation Lafiya Dole’ ta nemi haɗin kan ‘yan jarida

Daga FATUHU MUSTAPHA Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Major-General Faruk Yahaya, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su mara wa jami'an tsaro baya domin kawo ƙarshen Boko Haram a Nijeriya. Kwamandan ya yi wannan kira ne yayin wani taron karramawa da aka shirya wa 'yan jarida a Barno a barikin sojoji da ke Maimalari a jihar. General Yahaya ya nuna yabo tare da jinjina ga 'yan jarida inda ya bayyana su a matsayin masu taka muhimmiyar rawa a fagen yaƙi da ta'addanci da ake ci gaba da fafatawa. Ya ci gaba da cewa kafafen yaɗa labarai na da…
Read More
Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Jonathan ya ƙaddamar da hanya a Bauchi

Daga AISHA ASAS A Talatar da ta gabata Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ƙaddamar da babbar hanya ta farko wadda Gwamna Bala Mohammed ya gina a Bauchi. Hanyar wadda ta haɗa garin Sabon Ƙaura da ƙauyen Miri, na daga cikin hanyoyin farko-farko da gwamnan ya bada aikinsu a kwanaki 100 na farko da ya yi a kan mulki. Sa'ilin da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Bala ya ce sabuwar hanyar da aka gina mai nisan kilomita 6.2, an bada kwangilar ne kan kuɗi Naira bilyan N2. Daga nan, ya yaba wa Jonathan bisa ɗora shi kan hanya mai…
Read More

zamfara: ‘Yan sanda sun daƙile yunƙurin harin ‘yan bindiga

Daga WAKILINMU 'Yan sanda a jihar Zamfara sun daƙile yunƙurin harin 'yan ta'adda a ƙauyen Yarkala a gundumar Rawayya da ke cikin ƙaramar hukumar Bunguɗu a jihar. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar jami'in, jami'ansu sun sunkuya aiki ne bayan da suka samu labarin shirin da 'yan bindigar suka yi don kai hari a ƙauyen Yarkala a Alhamis da ta gabata. “Bayan da muka samu kira, ba a yi wata-wata ba sai jami'anmu suka dira a yankin inda suka daƙile shirin 'yan…
Read More

Sai da JAMB za a samu gurbin karatu a NDA – Hukumar Makaranta

Daga WAKILINMU Makarantar Horas da Sojoji ta Nijeriya (NDA) ta ce hankalinta ya kai kan wani rahoton ƙarya da ke ta karakaina a soshiyal midiya game da cewa an dakatar da JAMB a tsarin ɗaukar ɗalibai na '73 Regular Course'. Da wannan makarantar ta wayar da kan al'umma cewa lallai sai da shaidar jarabawar UTME za a iya samun gurbin karatu a '73 Regular Course', bayan kuma an samu adadin makin da hukumar JAMB ta tsayar. Daga nan, makarantar ta shwarci jama'a da su yi watsi da rahoton ƙaryar da aka yaɗa wanda ya nuna wai an dakatar da JAMB…
Read More