Labarai

Saudiyya ta tallafa wa ‘yan gudun hijira da abinci a Nijeriya

Saudiyya ta tallafa wa ‘yan gudun hijira da abinci a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Ƙasar Saudiyya ta bada tallafin kayan abinci na kuɗi Dalal bilyan $1.1 domin raba wa 'yan gudun hijira a jihar Barno da Yobe da Zamfara. Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da rabon kayayyakin a Talatar da ta gabata a birnin Maiduguri, Mataimakin Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Ibraheem Alghamedi, ya ce Sarki Salman ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu. Jakadan ya ce, “Ina mai amfani da wannan dama wajen jaddada kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Masarautar Saudiyya da Tarayyar Nijeriya. “Haƙika Saudiyya ta ƙuduri aniyar bunƙasawa da kuma…
Read More
Mutum biyu sun rasu a haɗarin hanyar Kaduna

Mutum biyu sun rasu a haɗarin hanyar Kaduna

An yi fargabar wasu mutum biyu sun mutu sakamakon wani mummunan haɗarin da ya faru a yankin Jere kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a wannam Litinin. Bayanan da Manhaja ta tattara sun nuna motoci biyun da haɗarin ya rutsa da su sun baro Abuja zuwa Kano ne inda akasin ya auku. Ya zuwa haɗa wannan labari, ba a bayyana dalilin aukuwar haɗarin ba. Tuni dai labarin aukuwar haɗarin ya isa ofishin jami'an kiyaye haɗurran kan haya mafi kusa.
Read More
Zanga-zanga: An hana lauyoyi shiga Majalisar Tarayya

Zanga-zanga: An hana lauyoyi shiga Majalisar Tarayya

Daga AISHA ASAS Jami'an tsaro a Abuja, sun hana tawagar lauyoyi da suka yi zanga-zanga shiga Majalisar Tarayya. A wannan Litinin mambobin Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) suka gudanar da zanga-zangar lumana zuwa Majalisar inda suka tarar da jami'an tsaro girke a ƙofar shiga majalisar. Manhaja ta gano cewa lauyoyin sun yin zanga-zangar ne domin nuna goyon baya da haɗin kai ga ma'aikatan fannin shari'a dangane da 'yancin gashin kan da suke nema na sarrafa kuɗaden gudanarwa. Tun farko sai da lauyoyin suka yi dafifi a ƙofar shiga Kotun Ɗaukaka Ƙara kafin daga bisani suka ɗunguma zuwa Majalisar Tarayya inda…
Read More
Za a soma gwanjon duk shanun da aka kama da lalata gona a Ondo

Za a soma gwanjon duk shanun da aka kama da lalata gona a Ondo

Daga WAKILINMU Gwamnatin jihar Ondo ta ce daga yanzu za ta riƙa gwanjon duk shanun da ta kama da laifin ɓarna a gona tare da hukunta masu shanun a bisa umarnin kotu. Shugaban 'yan bangan Amotekun na jihar, Cif Adetunji Adeleye, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar sakin shanu sama da 250 da Amotekun suka kama a Akure, babban birnin jihar. A cewar Adeleye Amotekun ta kama shanu sama da 250 a cikin jihar biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da manoman yankin Ipogun da Ilara da Owena Dam a ƙaramar hukumar Ifedore ta jihar suka…
Read More
Rikicin ƙungiyar asiri ya ci mutum shida a Ekiti

Rikicin ƙungiyar asiri ya ci mutum shida a Ekiti

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga jihar Ekiti sun tabbatar da mutuwar wasu mutum shida sakamakon rikicin da ya ɓarke a tsakanin ƙungiyoyin asiri a yankin Ikere na jihar. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar wa manema labarai da faruwar haka. Jami'in ya ce sun gano gawarwakin mutum shida da aka kashe sakamakon rikicin wanda ya auku da sanyin safiyar Lahadi. Wata majiya daga yankin da abin ya faru ta ce an ji ƙarar harbe-harben bindigogi yayin rikicin lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin gudun neman mafaka don tsira da rayuwarsu. Abutu ya ce waɗanda…
Read More
Boko Haram: Ministan Tsaro ya yi wa Jihar Borno tsinke

Boko Haram: Ministan Tsaro ya yi wa Jihar Borno tsinke

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Borno A ci gaba da kai ziyarar ƙarfafa gwiwa ga sojojin da ke aikin samar da tsaro a jihar Borno, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (ritaya), tare da Shugabanin Rundunonin Sojojin Nijeriya, sun yi wa birnin Maiduguri tsinke domin duba halin da ake ciki a yankin, a ranar Lahadi. Kwamandan shalkwatar Rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, Manjo Janar Farouq Yahaya, shi ne ya yi wa tawagar ministan marhabin, tare da yaba wa ƙoƙarin ministan da shugabanin sojojin dangane da ingantattun matakan da ministan tsaro tare da takwarorinsa ke ɗauka wajen ƙarfafa gwiwar rundunonin da ke…
Read More
Katsina: Za a tura karnuka don su bada tsaro a makarantu

Katsina: Za a tura karnuka don su bada tsaro a makarantu

Daga FATUHU MUSTAPHA A matsayin wani mataki na ƙokarin daƙile matsalar tsaro musamman ma a makarantun kwana, gwamnatin Jihar Katina ta amince da batun tura karnuka na musamman ya zuwa makarantun kwana domin su yi aiki tare da jami'an tsaro wajen bai wa makarantun kariya. Tun farko, sai da gwamnatin jihar ta ɗauki matakin tura jami'an tsaro biyar-biyar zuwa makarantun kwana tare da ɗaga katangar kariya domin samar da tsaro a makarantun da lamarin ya shafa a jihar. Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnati ta ɗauki matakin yin amfani da karnukan ne…
Read More
Taraba: Shugaban ƙaramar hukuma ya tsallake rijiya da baya

Taraba: Shugaban ƙaramar hukuma ya tsallake rijiya da baya

Daga UMAR M. GOMBE 'Yan bindiga sun kai wa Shugaban Karamar Hukumar Takum, Shiba Tikari, a jihar Taraba hari inda ya samu ya tsallake rijiya da baya. Harin wanda ya auku Asabar da ta gabata a ƙauyen Dogo-Gawa, ya yi sanadiyar rasa ran ɗan sandan da ke bai wa shugaban tsaro sakamakon wuta da tsegerun suka buɗe wa motocinsu. Manhaja ta gano cewa ɗan sandan da ya rasa ransa a harin na ɗaya daga cikin 'yan sandan kwantar da tarzoma su 67 da aka girke a yankin ƙaramar hukumar. A wata sabuwa, bayanai sun nuna 'yan sandan Ƙaramar Hukumar Wukari…
Read More
Adamawa: Buhari ya jajanta wa al’ummar Kwapre bisa harin ta’addanci

Adamawa: Buhari ya jajanta wa al’ummar Kwapre bisa harin ta’addanci

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa tare miƙa ta'aziyyarsa ga al'ummar Kwapre da ke yankin ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa, dangane da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai musu kwanan nan. Buhari a bisa wakilicin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya miƙa ta'aziyyarsa ne yayin ziyarar da sakataren ya kai a yankin da lamarin ya shafa. A cewar Boss Mustapha, "Na zo Kwapre ne a bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari domin ganin abin da ya auku. Shugaban ya jajanta muku kan abin da ya faru." Ya ce, "Na gani da idona irin ɓarnar da aka tafka…
Read More