Babban Labari

Wahalar fetur: Barazana ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

Wahalar fetur: Barazana ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

*Duk da gargaɗin DSS ƙarancin fetur na gurgunta harkokin rayuwa*’Yan Nijeriya sun koka da tsadar abinci da sufuri*Mun samar da miliyoyin ayyuka a fannin noma – Buhari Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu wahalar samun man fetur a Nijeriya cikin ’yan kwanakin nan yana matuƙar barazana ga samun walwala da jin daɗin al’ummar ƙasar a lokacin da suke ƙoƙarin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara mai kamawa ta 2023. A ranakun Lahadi da Litinin, 25 da 26 ga Disamba, 2022, za a gudanar da bikin ranar Kirsimeti, sannan kuma a ranar wata Lahadin ce za ta kasance…
Read More
Buhari ya kinkimo bashin tiriliyan N3 duk da tiriliyan N45 da ake bin gwamnatinsa

Buhari ya kinkimo bashin tiriliyan N3 duk da tiriliyan N45 da ake bin gwamnatinsa

Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sake kinkimo bashin Dalar Amurka biliyan $9 daidai da Naira tiriliyan 3.98 daga Bankin Duniya. Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Shubham Chaudhuri ne ya bayyana haka a wajen taron da ya shirya a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata. Shubham Chaudhuri ya ce, zaman Bankin Duniya a Nijeriya ba shi da burin da ya wuci taimaka wa ƙasar ficewa daga ƙangin talaucin da take ciki da kuma inganta rayuwar al'ummarta. A baya, jaridar Intel Region ta rawaito cewar, bashin da ake bin Nijeriya ya ƙaru zuwa Naira tiriliyan N45.8 ($103 billion) a…
Read More
Ɓatanci: Ganduje ya samu damar rataye Abduljabbar Kabara

Ɓatanci: Ganduje ya samu damar rataye Abduljabbar Kabara

*A gaggauta kashe ni, inji malamin*Yadda kotu ta yanke masa hukuncin kisa*An haramta karantawa ko sauraron wa’azinsa Daga BABANGIDA S GORA a Kano A ranar Alhamis ta jiya ne wata Babbar Kotun Shari'ar Musulunci da ta ke Ƙofar Kudu a cikin birnin Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ta bai wa Gamnan Jihar Kano izinin kashe Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ta hanyar rataya, wanda ta samu da hannu dumu-dumu kan furta kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) bayan kimanin shekara ɗaya da watanni biyar da gurfanar da shi a gabanta. Malam Abduljabbar, wanda kotun ta same…
Read More
Ɓatanci: Kotu ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa

Ɓatanci: Kotu ta yanke wa Abduljabbar hukuncin kisa

Daga WAKILINMU Kotun Shari'a a Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya. Kotu ta yanke wa malamin hukuncin kisa ne bayan da ta same shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW). Da yake yanke hukuncin, Alƙalin Kotun ya kuma buƙaci Gwamnatin Kano ta ƙwace masallatai guda biyun da ke ƙarƙashin kulawar Abduljabbar. Kazalika, Alƙalin ya yi kira da a daina sanya karatuttukan Abduljabbar ɗin a ɗaukacin kafafen yaɗa labarai, haka ma hotunansa. Bayan haka, kotun ta bai wa malamin wa'adin kwana 30 a kan ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa…
Read More
Gwamna Buni ya bayar da umurnin raba wa tsangayoyi 475 kayan abinci da tufafi a Yobe

Gwamna Buni ya bayar da umurnin raba wa tsangayoyi 475 kayan abinci da tufafi a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu A ƙoƙarin sa na inganta rayuwar al'ummar jihar, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, umurnin raba wa makarantun tsangaya 475, wanda ake sa ran alarammomi da almajiransu 8,000 za su ci gajiyar tallafin kayan abinci da na masarufi haɗi da dilolin tufafin sakawa, barguna, tabarmin leda, bokitan ruwa da sauran su a faɗin jihar Yobe. Da take ƙaddamar da rabon tallafin a Tsangayar Slaramma Goni Yahaya dake unguwar Gwange a Damaturu, Sakataren Hukumar SEMA, Dr. Muhammad Goje, wanda Daraktan hukumar, Alhaji Hassan Bomai ya…
Read More
Jirgin Abuja-Kaduna: Za a hana yin waya a jirgin ƙasa

Jirgin Abuja-Kaduna: Za a hana yin waya a jirgin ƙasa

*An soke zirga-zirgar dare*Akwai tsare-tsare na sarari da ɓoye – Ministan Sufuri*Za a ƙara kuɗin tikiti da albashin ma’aikata, inji Ministan Sufuri*Ni da iyalina za mu riƙa hawa jirgin saboda tabbacin tsaronsa, inji Ministan Ruwa*Mu na aiki kan samar sababbin manufofi – Shugaban Hukumar Daraktoci Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, akwai yiwuwar ta hana amfani da waya a cikin jiragen ƙasan Abuja zuwa Kaduna, wanda aka dakatar da zirga-zirgarsu tun bayan harin da aka kai wa jirgin fasinjojin a cikin watan Maris da ya gabata. Shugaban Hukumar Daraktoci na Kamfanin Sufurin Jiragen Ƙasa…
Read More
2023: Ba za a sake barin gwamnoni hana ’yan adawa taro ba – Sufeto Janar

2023: Ba za a sake barin gwamnoni hana ’yan adawa taro ba – Sufeto Janar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba Alƙali, ya bayyana cewa, babu wani gwamna da za a sake bari ya hana jam’iyyun siyasa na adawa gudanar da taro a jihohinsu. IGP Baba ya yi wannan maganar ne ranar Laraba a taron jam’iyyun siyasa na 2022 a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya. Sufeto Janar ɗin, wanda ya samu wakilcin Dandaura Mustapha, Mataimakin Sufeto Janar na Hukumar ’Yan Sanda (DIG), ya ce, an umarci kwamishinonin jihohi da su tabbatar an bai wa kowane ɓangare damar gudanar da yaƙin neman zaɓe. Baba ya ƙara da cewa, yayin da…
Read More
Gwamnoni sun ƙalubalanci Buhari ya bayyana sunayen gwamnonin da ke wawushe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Gwamnoni sun ƙalubalanci Buhari ya bayyana sunayen gwamnonin da ke wawushe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu gwamnonin sun ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya bayyana sunayen gwamnonin jihohin da ya zarga da satar kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomin jihohinsu duk wata. Idan za a iya tunawa cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya zargi wasu gwamnoni da wawushe kuɗaɗen da ke tura wa ƙananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya. Ya koka da yadda gwamnonin ke yi wa matakin ƙananan hukumomi rashin adalci. Shugaban ya yi tsokaci ne kan ‘ayyukan damfara’ da wasu gwamnoni suka yi wajen rabon kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da ƙananan hukumomi. Ya ce, ba za…
Read More
Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibi Aminu

Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibi Aminu

Daga BASHIR ISAH Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibin nan Mohammed Aminu bayan da ta sha caccaka da tofin Allah wadai daga ɓangarori daban-daban. Lauyan Aisha, Fidelis Ogbobe ya ce Aisha ta janye ƙarar ne bayan da wasu manyan ƙasa suka sa baki cikin batun. Ya ce ta janye ƙarar ne ta hanyar kafa hujja da Sashe na 108 da ƙaramin sashe na 2(a) na Dokar Manyar Laifuka. Da yake yanke hukuncin kan batun, Alƙalin Babbar Kotun, Mai Shari'a Yusuf Halilu, ya yaba wa Aisha Buhari dangane da haƙuri da afuwar da ta…
Read More
Gwamnoni da ciyamomi na wawushe kuɗaɗen da aka ware wa kansiloli – Buhari

Gwamnoni da ciyamomi na wawushe kuɗaɗen da aka ware wa kansiloli – Buhari

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa, gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomin ƙasar nan na sace kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya take ware wa kansiloli. Wannan na zuwa ne kimanin sa'o'i 24 bayan da Ƙaramin Ministan Kuɗi, Mr. Clement Agba, ya zargi gwamnoni da jefa jihohinsu cikin talauci ta hanyar mayar da yankunan karkara saniyar ware a harkokinsu. Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja, Agba ya ce gwamnonin sun maida hankali wajen gina filayen jirgin sama da gadojin sama a biranesu maimakon yi wa yankunan karkara hidima. A nasa ɓangaren, Shugaba Buhari ya faɗa…
Read More