Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibi Aminu

Daga BASHIR ISAH

Matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da ta shigar kan ɗalibin nan Mohammed Aminu bayan da ta sha caccaka da tofin Allah wadai daga ɓangarori daban-daban.

Lauyan Aisha, Fidelis Ogbobe ya ce Aisha ta janye ƙarar ne bayan da wasu manyan ƙasa suka sa baki cikin batun.

Ya ce ta janye ƙarar ne ta hanyar kafa hujja da Sashe na 108 da ƙaramin sashe na 2(a) na Dokar Manyar Laifuka.

Da yake yanke hukuncin kan batun, Alƙalin Babbar Kotun, Mai Shari’a Yusuf Halilu, ya yaba wa Aisha Buhari dangane da haƙuri da afuwar da ta yi tare da janye ƙarar zargin da ɗalibi Aminu ya yi mata.

Daga nan, Alƙalin ya yi jan hankali kan iyaye su riƙa kulawa da ‘ya’yansu yadda ya kamata gudun sake aukuwar makamancin abin da Aminu ya aikata.

Aisha ta maka ɗalibin a kotu ne kan zargin ɓata mata suna.

Aminu wanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ya ci na jaki a hannun jami’an tsaro bayan da suka kama shi suka tafi da shi Abuja.

Kalaman sukar Aisha kan ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi sanadiyar aka kama ɗalibin ran 18 ga Nuwamba a makarantarsu.