Hukumar EFCC za ta fara gwanjon motocin da ta ƙwace

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta sanar da yin gwanjon motoci sama da 800 da sauran kayayyakin da ta ƙwace a hannun waɗanda ake zargi a aikata laifi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Juma’a 2 ga watan Disamba, 2022.

A cewar sanarwar, hukumar ta ce, za a yi gwanjon ne a faɗin ofisoshin shiyya-shiyya da ke faɗin ƙasar nan. Ya ƙara da cewa, a duk ranar gwanjon, za a fara aikin ne daga ƙarfe 9 na safe zuwa 3 na yamma.

“Ana sanar da jama’a cewa Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta hannun wanda aka naɗa mai gwanjon kaya za ta gudanar da gwanjon kayayyakin da ba a lissafa ba waɗanda ke ƙarƙashin umarnin ƙwacewa kamar yadda dokar EFCC ta 2004 ta tanada,” inji sanarwar.

Hukumar ta bayyana cewa ba a buɗe kasuwar gwanjon ne ga ma’aikatanta, ’yan fansho da kuma waɗanda aka su ka yi asarar kadarorinsu.