27
Jan
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin matsalar ƙarancin man fetur da ake fuskanta da sauya fasalin wasu takardun Naira da aka yi, take-taken neman wargaza zaɓen 2023 ne kawai. Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yaqin neman zaɓen APC da ya gudana ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. “Ba sa son zaɓen ya gudana. So suke su wargaza shi. Za ku bari hakan ta faru?” inji Tinubu. Ɗan takarar ya ce, yana da yaƙinin matsalar ƙarancin fetur ba za ta hana ’yan Nijeriya zuwa kaxa…
