14
Feb
*Ya ce duk mai tsohon kuɗi ya kai CBN Daga AISHA ASAS Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da kuma N1000 sun daina amfani a hukumance tun daga ran 10 ga Fabrairu, 2023. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban CBN a Bauchi, Haladu Idris Andaza, yayin zantawarsa da manema labarai ranar Litinin a garin Bauchi. Ya ce, “A tsakanin awowi 24 da suka gabata, mun samu tambayoyi da yawa daga wajen mutane game da batun tsoffin kuɗi." A cewarsa, "domin kawar wa jama'a shakku, muna sanar da cewa a shirye CBN yake…
