Babban Labari

Zaɓen 2023: Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa

Zaɓen 2023: Buhari ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da mai ɗakinsa, Aisha, gami da sauran ahalinsa sun kaɗa ƙuri'arsu a rumfar zaɓe ta 003, a Sarkin Yara A, Ƙofar Baru da ke Daura, Jihar Katsina. Bayanai sun nuna Shugaba Buhari da ahalin nasa sun isa rumfar zaɓen ne da misalin ƙarfe 9.57 na safe. Ba da ɓata lokaci ba aka tantance Buhari kana aka ba shi damar kaɗa ƙuri'arsa. Buhari ya yi kira da a yi zaɓe cikin lumana kana 'yan takara kowa ya yarda da sakamakon zaɓen bayan kammalawa.
Read More
Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

*Addinanci, ƙabilnci da ɓangaranci ba baqi ne a siyasar Nijeriya ba!*Shin za a iya zuwa zagaye na biyu? Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A gobe Asabar ne za a gudanar da Babban Zaɓe a Nijeriya bayan shafe kusan shekaru huɗu na zango na biyu da shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, ya yi a kan kujerar mulkin ƙasar. Kowane zaɓe ya kan zo da yanayinsa kuma ya kan sha bamban da na bayansa. Siyasar addinanci da ɓangaranci ko ƙabilanci ba baƙin abubuwa ba ne a Nijeriya. Don haka ba su daga cikin abubuwan da zaɓen 2023 ya bambanta da na…
Read More
2023: An cafke shugabannin ƙananan hukumomi biyu da bindigogi a Kano

2023: An cafke shugabannin ƙananan hukumomi biyu da bindigogi a Kano

*’Yan daba sun farmaki magoya bayan Kwankwaso Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An cafke wasu shugabannin ƙananan hukumomi guda biyu na Jihar Kano sakamakon zargin da ake yi na kama su bindigogi da aka yi a yayin gangamin siyasa jiya, Alhamis. Bugu da ƙari, wasu ’ƴan daba da ake kyautata zaton ’ƴan bangar siyasa ne, sun farmaki magoya bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar adawa ta NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, a Jihar Kano. Rahotonni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a unguwar Na’ibawa da ke kan titin zuwa Zariya. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, yayin farmakin, magoya…
Read More
Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya isa Jihar Katsina, inda daga nan ne zai zarce zuwa Daura, mahaifarsa, domin halartar zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi gobe Asabar.Jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Umar Musa Yar’Adua da misalin ƙarfe 4:40 na yammacin jiya Alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023. A gobe Asabar ne ake sa ran zai kaɗa ƙuri’arsa ga ‘yan takarar da yake so a Daura. Kafin ya bar Abuja zuwa Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Buhari ya kira taron majalisar tsaro, inda ya…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun cafke ɗan majalisa ɗauke da $500,000 a Ribas

Da ɗumi-ɗumi: ‘Yan sanda sun cafke ɗan majalisa ɗauke da $500,000 a Ribas

Daga WAKILINMU 'Yan sanda a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, sun cafke ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Chinyere Igwe, da safiyar Juma'a ɗauke da kuɗi sama da Dala dubu 500 ($500,000.00), yayin da ya rage sa'o'i 24 kafin zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisar tarayya a Nijeriya. Binciken Blueprint Manhaja ya gano cewa, kuɗin da aka kama Igwe da shi ana zargin ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya ba shi tare da wata takarda mai ɗauke da sunayen ƙananan hukumomi 23 na jihar da hukumomin tsaro da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). Sai dai…
Read More
Canjin kuɗi: Kotun Ƙoli ta tafi hutu

Canjin kuɗi: Kotun Ƙoli ta tafi hutu

Daga WAKILINMU Kotun Ƙoli mai sauraron shari’ar sauyin kuɗi tsakanin gwamnatocin jihohi 13 da Gwamnatin Tarayya ta tafi hutu. Alƙalan kotun su bakwai ƙarƙashin Mai Shari’a Inyang Okoro sun ce sun tafi hutu domin bai wa lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar damar yin musayar takardu. Hakan na zuwa ne bayan Jihar Ribas ta shiga jeri a matsayin ta 13 a cikin jihohin da ke ƙalubalantar sauyin kuɗin da gwamnati ta yi. Tun da farko, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce ya zama tilas kotun ta cimma matsaya a kan shari’ar a zamanta na yau. Wannan shi ne zama na biyu…
Read More
Yadda mai juna-biyu ta rasu a asibitin Nasarawa…saboda ƙin karɓar tsohon kuɗi a Kano

Yadda mai juna-biyu ta rasu a asibitin Nasarawa…saboda ƙin karɓar tsohon kuɗi a Kano

*Mijinta ya zayyana yadda lamarin ya faru*Mun fara bincike kan lamarin, inji hukumar asibitocin jihar*Gwamnatin Tarayya ce ta saka ’yan Nijeriya a cikin matsalar – Gwamnatin Kano Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Wata mai juna-biyu, Malama Shemau Sani Labaran, ta rasa ranta a lokacin da ta ke naquda sakamakon ƙin karɓar tsofaffin takardun kuɗi da asibitin Nasarawa dake Jihar Kano ke yi, kamar yadda mijinta, Bello A. Baffancy, ya tabbatarwa da Blueprint Manhaja. Idan dai za a iya tunawa, harkokin rayuwa su na samun cikas a Nijeriya sakamakon canjin fasalin Naira 200, 500 da 1,000 da Babban Bankin Nijeriya…
Read More
Lalata takardun Naira 200: Emefiele ya gana da shugabannin bankuna

Lalata takardun Naira 200: Emefiele ya gana da shugabannin bankuna

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da ake tsaka da yaɗa rahotanni game da cewa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya lalata  takardun tsofaffin kuɗi na Naira 200, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya je don ganawa da shugabannin zartarwa na bankunan Nijeriya.  Idan za a iya tunawa, Shugaban Ƙasa  Muhammadu Buhari ya yi jawabin da ya sanar da 'yan Nijeriya cewa, ya bayar da damar a cigaba da amfani da tsofaffin takardun Naira 200 har zuwa nan da kwanaki 60. Buhari ya bayyana cewa, ya bayar da wannan umarnin ne, saboda sauƙaƙa wa mutane wahala, wanda shi ya sa ya ba…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: CBN ya umarci bankuna su karɓi N500 da N1000

Da ɗumi-ɗumi: CBN ya umarci bankuna su karɓi N500 da N1000

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna su fara karɓar tsoffin takardun N500 da N1,000 daga hannun jama'a nan take. Sai dai, CBN ya sharɗanta cewa Naira 500,000 ita ce mafi girman abin da bankunan za su karɓa amma ban da abin da ya haura haka. Majiyarmu ta ce CBN ya ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙe wa jama'a wahalar zuwa rassan CBN a faɗin ƙasa don mayar da tsofaffin kuɗin. Wani jami'in CBN ya ce, "Ku tafi bankunanku, amma ku tabbatar kun cike fom kafin ku tafi. Ku je da kebaɓɓun lamɓoɓin da kuka samu. "Bankuna…
Read More
Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Buhari ya tsawaita wa’adin tsohuwar N200

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince a ci gaba da amfani da tsohuwar N200 nan da wata biyu. Ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan ƙasa kai tsaye da safiyar Alhamis. Buhari ya ce ya tsawaita wa'adin amfani da N200 ne domin rage wa 'yan ƙasa raɗaɗin ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a faɗin ƙasa. A cewarsa, za a ci gaba da amfani da N200 ne daga ran 10 Fabrairu zuwa 10 ga Afrilun 2023. Sai ƙarin wa'adin in ji Buhar, bai shafi tsoffin N500 da N100 ba. Shugaban ya ce ƙofar CBN…
Read More