Babban Labari

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tsawaita wa’adin tsoffin kuɗi zuwa Disamba

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tsawaita wa’adin tsoffin kuɗi zuwa Disamba

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200 da N500 da kuma N1000 har zuwa 31 ga Disamban 2023. Kotun ta ce tsoffin kuɗin za su ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da sabbin da aka samar. A ranar Juma'a, Kotun, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Inyang Okoro ta ba da wannan umarni inda ta ce umarnin sauya Naira 200, 500 da 1000 da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Bankin Ƙasa (CBN) ba tare da ya tuntuɓi jihohi da Majalisar Zartarwa da Majalisar Tsoffin Shugabannin Ƙasa ba, hakan…
Read More
A shirye nake mu haɗu a kotu, martanin Tinubu ga Atiku

A shirye nake mu haɗu a kotu, martanin Tinubu ga Atiku

Daga BASHIR ISAH Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Ahmed Tinubu, ya ce a shirye yake su fafata a kotu tare da ɗan takarar Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, kan ƙarar da ya ce zai shigar. Da yake jawabi yayin taron manema labarai a ranar Alhamis, Atiku ya yi zargin ba a yi adalci ba a zaɓen da ya gudana Asabar da ta gabata wanda hukumar INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara. Da yake maida martani ta bakin Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Festus Keyamo (SAN), Tinubau ya ce, “A shirye yake wa ƙalubalantar sakamakon zaɓen da Atiku ya…
Read More
Zaɓen 2023: Za mu ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu – LP

Zaɓen 2023: Za mu ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu – LP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar Labour Party (LP) mai adawa a zaɓen Shugaban Ƙasa na Nijeriya ta bayyana cewa za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen da ya bayyana Bola Tinubu na Jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara. Yayin da yake jawabi a Abuja a ranar Laraba, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar LP, Datti Baba Ahmed, ya jaddada cewa akwai kura-kurai a zaɓen. "Mun shiga zaɓen a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP," a cewarsa. "Kuma za mu ƙwaci haƙƙinmu da sunan LP". Tun a ranar Talata jam'iyyun adawa na PDP…
Read More
Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa da mataimakinsa sun ziyarci Buhari a Katsina

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa da mataimakinsa sun ziyarci Buhari a Katsina

Daga BASHIR ISAH Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun bi Shugaba Buhari da shaidar lashe zaɓen da INEC ta miƙa musu har Daura don tayaurna da kuma sanya musu albarka. Tinubu da Shettima sun wannan ziyarar ne bisa rakiyar Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu. Sauran 'yan rakiyar sun haɗa da Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna), Atiku Bagudu (Kebbi), Dave Umahi (Ebonyi), Bello Matawalle (Zamfara), Abubakar Sani-Bello (Neja), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), Badaru Abubakar (Jigawa) da kuma Simon Lalong (Filato). Sabon zaɓaɓɓen shugaban ya yi amfani da wannan dama wanen nuna…
Read More
Tinubu ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa

Tinubu ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa

*Yau za a miƙa masa takardar shaida Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zama sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya. Tinubu ya yaki wannan matsayi me biyo bayan zaɓaɓɓen da aka gudanar a ƙasar ran Asabar da ta gabata. Yau Laraba ake sa ran Hukumar INEC za ta miƙa wa Tinubu shaidar lashe zaɓaɓen da ya yi. Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ha ba da sanarwar nasarar da Tinubu ya samu, tare da cewa za a miƙa masa shaidar ne da misalin ƙarfe 3 na ranar a Babban Zauren Taro…
Read More
Buhari ya gargaɗi Obasanjo kan yi wa  sha’anin zaɓe shisshigi

Buhari ya gargaɗi Obasanjo kan yi wa sha’anin zaɓe shisshigi

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kada ya haifar wa zaɓen 2023 da tasgaro da wasiƙar da ya rubuta na tada zaune tsaye da son-kai da tada hankali kan zaɓe. A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce abin da tsohon Shugaban ƙasar ya yi ba komai ba ne illa ƙoƙarin haifar da cikas ga tsarin zaɓe da kuma yin magudin zaɓe da tada hankali. Obasanjo ya ce babu nagarta a babban zaɓen ƙasar da aka yi ranar Asabar don haka ya ce…
Read More
NNPP ta buga ɗan gidan Ganduje da ƙasa, ta lashe zaɓen ɗan majalisa a Kano

NNPP ta buga ɗan gidan Ganduje da ƙasa, ta lashe zaɓen ɗan majalisa a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Abba Abdullahi Umar Ganduje, ɗa a gurin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya faɗi zaɓen ɗan majalisar wakilai a Kano. Ɗan gidan gwamnan wanda ya fito takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓun Tofa da Rimingado, ya sha ƙasa bayan da abokin karawarsa Tijjani Abudlkadir Jove, ɗan takarar jam'iyyar NNPP ya buga ahi da ƙasa. Jove wanda shi ne wakilin riƙon ƙwarya na wakilcin majalisar, zai maimaita kujerar tasa ne a karo na biyar. An kaɗa wa Jove ƙuri'u 52, 456 yayin da Abba Ganduje shi kuma ya samu ƙuri'u 44,809.
Read More
Mutum 3 sun mutu a harin da aka kai ofishin NNPP a Kano

Mutum 3 sun mutu a harin da aka kai ofishin NNPP a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum biyu yayin da ake tsaka da tattara sakamakon zaɓe a ƙaramar hukumar Tudun Wada dake jihar kano. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Kano, CP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin. Sanarwar ta ce an sami bayanai cewa ana cikin tattara sakamakon zaɓen a Tudun Wada ne cikin ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar wasu gungun 'yan dabar siyasa suka kai hari a ofishin kamfen na ɗan takarar majalisar tarayya tare da cinna masa…
Read More
Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilinsa na kaɗa wa Asiwaju TInubu ɗan takarar shugaban ƙasa a jamiyyar APC ƙuri'a a bainan nasi a yayin da yake zaɓe a mahaifarsa wato Daura. Shugaban ya bayyana cewa, ba wani abu ne ya sa ya bayyana zaɓinsa ga Tinubun ba illa nuna biyayyarsa da goyon bayansa gare shi. A cewar sa, bayan ya kewaye lungu da saƙo na ƙasar nan don yin yaƙin neman zaɓe ga tsohon gwamnan na Legas, ya kamata ya cika aikinsa na jaddada goyon baya a gare shi a matsayin wanda ya fi so…
Read More