10
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana dalilinsa na ƙaurace wa taron miƙa wa zaɓaɓɓun sanatoci takardar shaidar lashe zaɓen da aka gudanar a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, a makon nan. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Malam Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a ƙarƙashin jtsohuwar jam’iyyarsa ta NNPP maimakon jam’iyyarsa ta yanzu, PDP. Sai dai ɗan majalisar mai ci bai halarci taron miqa takardar shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun sanatocin ba a ranar Talatar da ta gabata.…
