16
Mar
15
Mar
Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya (NBS), ta ce aƙaluman rashin aiki a Nijeriya sun sake cillawa, kamar yadda wani rahotanta ya nuna bada jimawa ba. Rahoton hukumar ya nuna an samu ƙarin adadi na rashin aiki a Nijeriya da ya kai kashi 33.3 cikin ɗari a zango na huɗu a 2020 saɓanin kashi 27.1 cikin ɗari a zango na biyu a 2020. NBS ta sanar da haka ne a cikin rahotonta da ta shirya kan sha'anin ƙwadago, tare da la'akari da matsalar rashin aiki musamman kuma a zamanin da ake fama da cutar korona, inda ta gano…
15
Mar
Daga UMAR M.GOMBE Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce babbar manufar Shugaba Muhammadu Buhari na gina layin dogo a sassan ƙasa ita ce don samar da aikin yi ga matasan Nijeriya. A Lahadin da ta gabata Minista Amaechi ya bayyana haka ta hannun hadimarsa kan sha'anin yaɗa labarai, Mrs Taiye Elebiyo-Edeni, yana mai cewa ayyukan samar da hanyoyin jirgin ƙasa da ke kan gudana za su taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce, bayan kammala layin dogo da ake ginawa a gabashin ƙasa hakan zai zama silar samar da gurbin aiki tsakanin 20,000 zuwa 50,000 baya ga sauran harkokin…
14
Mar
Daga WAKILINMU 'Yansandan Jihar Ogun sun cafke wata mata 'yar shekara 43 mai suna Bisola Awodele bayan da ta babbaka mijinta da tafasasshen ruwa, lamarin da ya yi wa mijin nata mummunan rauni a baya. Sanarwar manema labarai da Jami'in Hulɗa da Jama'a na 'yansandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar a Abeokuta a ranar Lahadi, ta nuna Bisola ta faɗa a komar hukumar ce ranar 8 ga Maris biyo bayan rahoton da magidanta mai suna Peter Philip, ya kai a ofishin 'yansandan na yankin Sango Ota. Peter ya shaida wa 'yansandan cewa matarsa na zarginsa da yawan shan giya…
13
Mar
Sabuwar Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO) Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta iso Nijeriya inda ake sa ran za ta shafe mako guda. Daga bayanan da Manhaja ta kalato, kai ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari na daga cikin harkokin da Ngozi za ta aiwatar domin nuna godiyarta ga irin rawar da Buhari ya taka wajen ganin ta sami ɗarewa sabon muƙamin nata. Okonjo-Iweala ta ce yayin ziyarar tata, za ta tattauna da Shugaba Buhari tare da sauran masu ruwa da tsaki game da irin tanadin da WTO ta yi wa tattalin arzikin Nijeriya a matsayinta na shugabar hukumar.
12
Mar
An fitar da matakan da masu shiga shirin za su bi Daga WAKILIN MU Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen dogon jiran da ake yi na fara aiwatar da rukuni na uku (Batch C) na shirin N-Power wanda za a shigar cikin jerin shirye-shiryen rage matsin rayuwa, wato National Social Investment Programmes (NSIPs). Mai bada shawara kan aikin jarida ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Madam Nneka Ikem, ita ce ta bayyana haka a ranar Alhamis cikin wani saƙo da ta tura a Twitter. A cewar ta, ana kira ga dukkan waɗanda su ka cike takardun nema shiga shirin…
11
Mar
Daga WAKILINMU Majalisar Wakilai ta Ƙasa, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta maida kuɗaɗen da Ibori ya sata, Pan milyan £4.2, ga Jihar Delta. Wannan ya biyo bayan ƙudirin da 'yan majalisar daga jihar Delta suka gabatar wa majalisar ne a Larabar da ta gabata. Haka nan, 'yan majalisar sun ce jimillar kuɗin Pan miliyan £6.2 ne amma ba milyan £4.2 ba kamar yadda aka ruwaito. Bugu da ƙari, Majalisar ta buƙaci Ma'aikatar Kuɗi ta Kasa da ta bai wa Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, umarnin ya miƙa wa Majalisar dukkan takardun da ke da alaƙa da…
10
Mar
Daga BASHIR ISAH Gwamnan Nasarawa Engineer Abdullahi Sule, ya ƙaddamar da allurar rigakafin cutar koron inda shi da mataimakinsa, Dr. Emmanuel Akabe, suka soma yin rigakafin na Oxford-AstraZeneca. Bikin ƙaddamarwar ya gudana ne ranar Talata a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia, babban birnin jihar. Da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan ya yi allurar, Gwamna Sule ya yi kira ga 'yan jiharsa, musamman ma waɗanda suka fi fuskantar haɗarin harbuwa da cutar kamar 'yan siyasa da sarakunan gargajiya da sauransu, da su tabbatar sun yi allurar. Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen nuna godiyarsa…
10
Mar
Daga UMAR M. GOMBE Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada sammaci wanda ya tilasta wa Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami SAN, da tsohon shugaban riƙo na hukumar EFCC Ibrahim Magu, da su bayyana a gabanta. Kotu ta buƙaci ganin waɗanda lamarin ya shafa ne domin su bada shaida a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina. Kazalika, kotun ta umarci Shugaban Babban Bankin Ƙasa (CBN), Godwin Emefiele da wasu da su bayyana a gabanta a ranakun 9, 10 da 11 na Maris domin bada shaida. Sauran mutanen da…
10
Mar
Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta yarda 'yan kasuwa su shigo da allurar rigakafin cutar korona ba, tare da cewa dole dukkan rigakafin da za a shigo da su ya kasance ta hannun gwamnati. Ƙaramin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora ya faɗi haka ran Talata a Abuja.Ministan ya ce 'yan Nijeriya masu bukatar a yi musu rigakafin korona sai su yi rajista a shafin intanet na Hukumar Kula da Lafiaya a Matakin Farko. Mamora ya ce a halin yanzu ba a yarda 'yan kasuwa su soma harkar shigo da allurar rigakafin korona ba. Ya ce gwamnati ba za…
