Adabi

Bayan nasarar littafin ‘Orbital’ a gasar marubuta ta Booker Prize a duniya

Bayan nasarar littafin ‘Orbital’ a gasar marubuta ta Booker Prize a duniya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Na fara karanta labarin 'Tattaki Cikin Zamunna' wanda Farfesa Yusuf Muhammad Adamu na Jami'ar Bayero ta Kano ya wallafa ne tun a tsohuwar jaridar Nasiha wacce ake bugawa a Kaduna, wacce a lokacin take tsakuro labarin ana bugawa mako-mako. Kodayake a lokacin ina makaranta, ban yi zurfi wajen nazarin ilimin 'Time Traɓel' sosai ba. Sai dai salon marubucin na ƙirƙirar labari da salon rubutu na 'Science Fiction', wanda ba kasafai za ka ga irin sa a rubutun 'yan Afirka ba, ballantana ma a yi batun marubutan Hausa, ya daki tunanina sosai. Har yanzu idan na ɗauki…
Read More
Har yanzu ba a daina yayin littattafaina ba – Hafsat C. Sodangi

Har yanzu ba a daina yayin littattafaina ba – Hafsat C. Sodangi

"Ina rubutu ne don samun natsuwa a zuciyata" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Ga duk waɗanda suka karanta littattafan Hausa a wajejen farkon shekarun 2000 zuwa 2010 ba za su kasa karanta littattafan Hafsat C. Sodangi ba, wata marubuciya daga garin Jos. Hajiya Hafsat Sodangi ta yi fice wajen rubuta ƙirƙirarrun labarai da suka shafi zamantakewar ma'aurata, soyayya da kishi a tsakanin mata. Tana daga cikin marubutan da suka ci gajiyar rubutu a shekarun baya, kuma a yanzu ma da galibin marubuta suka koma rubutu ta onlayin, littattafanta suna cigaba da samun karɓuwa. Kawo yanzu marubuciyar ta rubuta littattafai aƙalla 31,…
Read More
Ma’anar  sara

Ma’anar  sara

Daga MUHAMMED BALA GARBA  Sara wani irin salo ne na magana da ke ƙunshe da ƙirƙirarrun zantuka waɗanda kan yi tashe ko yayi a wani lokaci. Waɗannan zantuka sukan ba da ma'ana ta musamman ga wanda ya san su. Wani lokaci yayin wata sara yakan wuce, sai wani sabo ya shigo. Wani lokacin kuma akan samu Sarar da kan jima ba a manta da ita ba, ko da kuwa an samu wata sabuwa ta zo a bayanta. Haka nan kuma, sara na iya nufin wani yayi ko salo na yin magana da abokai ke yi a tsakaninsu wanda ya gama…
Read More
Zama marubuci hanyace mai sauƙi idan har da sha’awa – Maryam Nuhu Turau 

Zama marubuci hanyace mai sauƙi idan har da sha’awa – Maryam Nuhu Turau 

"Tun ina makarantar firamare na fi sauran ɗalibai iya karatun litattafan Hausa" Daga UMAR GARBA a Katsina  Maryam Nuhu Turau kallabi ce tsakanin rawuna duba da cewa ta yi fice a zahiri da kuma kafafen sada zumunta na zamani, saboda kasancewarta marubuciya, 'yar kasuwa kuma mai bai wa matasa shawara akan su nemi na kansu. Ta kuma kasance uwa wadda ta kafa ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin marubuta a arewacin ƙasar nan. Wakilin Blueprint Manhaja a Katsina, Umar Garba ya tattauna da Maryam Nuhu Turau a kan batutuwan da suka shafi harkar rubutu, kasuwanci, shawara ga matasa, ƙalubalen da ta…
Read More
Ina da burin taimaka wa ƙananan mawaƙa da marubuta – Aliyu Al’usku 

Ina da burin taimaka wa ƙananan mawaƙa da marubuta – Aliyu Al’usku 

(Ci gaba daga makon jiya) Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU MANHAJA: Waɗanne nasarori ko ƙalubale aka fuskanta kawo yanzu, a cikin harkokinka na waƙa?  AL'USKU: Na samu nasarori masu yawa da ba zan iya lissafa su ba, na samu karramawa da kyautuka masu yawa daga masoya da na sani da waɗanda ban sansu ba ma. Alhamdulillah.  Batun ƙalubale fa?  To, Alhamdu Lillah, babu wani abu na alkhairi da babu ƙalubale a cikinsa. Game waɗannan ayyukan rubutawa da rera waƙoƙi da nake yi, na fuskance su iri daban daban. Ba alfahari ba, kamar yadda duk masu bibiyar waƙoƙina suka sani, na fi…
Read More
Ba zan iya rubuta waƙa ba har sai na yi bincike – Aliyu Al’usku 

Ba zan iya rubuta waƙa ba har sai na yi bincike – Aliyu Al’usku 

Na gaje waƙa ne a wajen mahaifina Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Duk wani manazarcin adabi na sane da muhimmancin waƙa wajen raya al'adu da tasirinta ga ilimantar da jama'a. Don haka alaƙar waƙa da rubutu da wasan kwaikwayo take da tsohon tarihi, ba a ƙasar Hausa kaɗai ba, har ma da dukkan al'adu da ake nazarinsu a cibiyoyin ilimi. Malam Aliyu Usman Kuringafa, wanda aka fi sani da Aliyu Al'usku, ba ɓoyayye ba ne a fagen rubutawa da rera waƙoƙi cikin fasaha da zalaƙar harshe. A tattaunawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, mawallafin ya bayyana masa cewa shi…
Read More
Nasarar murubuciya Han Kang a duniya: Ƙalubalen marubutan Arewa

Nasarar murubuciya Han Kang a duniya: Ƙalubalen marubutan Arewa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Har yanzu duniya na cigaba da tattaunawa tare da yabawa da nasarar da wata marubuciya 'yar ƙasar Koriya ta Kudu mai suna Han Kang ta samu a Gasar Fitattun Mutane ta duniya, wanda aka fi sani da Nobel Prize, wacce a bana aka yi nazari kan Rubutun Adabi, yayin da littafinta mai suna 'The ɓegetarian' ya zama na ɗaya. Littafin da ya taɓa samun nasara a Gasar Man Booker International Prize a shekarar 2016. Littafi ne da yake ɗauke da labarin wata mata Yeong-hye wacce ta yi wa cin nama tawaye, sai dai hatsi da 'ya'yan…
Read More
Me ya sa mu ke gudun sunayen Hausa na gargajiya?

Me ya sa mu ke gudun sunayen Hausa na gargajiya?

Daga FARFESA ABDALLA UBA ADAMU Illar Cancel Culture!  Kwanakin baya na yi rubutu da Ingilish a kan sunayen Hausawa na gargajiya. Mutane da dama sun nema in fassara zuwa Hausa domin ƙaruwar al’umma. To gashi nan! Kusan shekaru 45 da suka wuce, matar wani amini na ta haifar mu su da ɗa. Aminin nawa ya ce da magabantan sa a sawa yaron suna Maikuɗi. Duka ɓangaorin – na matar sa da na sa – suka tirje kan cewa ai ‘Maikuɗi’ ba suna ba ne. Shi kuma bai ga wani aibu da sunan ba, tunda sunan gargajiya ne na Hausawa. Kuma…
Read More
Rubutu a soshiyal midiya ya taimaka wa marubuta da yawa – Zaidu Barmo 

Rubutu a soshiyal midiya ya taimaka wa marubuta da yawa – Zaidu Barmo 

Tun Ina firamare na fara rubutu Daga UMAR GARBA, a Katsina Zaidu Ibrahim Barmo matashi ne da ya yi fice a fannoni daban daban, kama daga rubutun litattafai ko labarai a mujallu da jaridu gami da yin sharhi game da rayuwar matasa a kafafen yaɗa labarai. Kazalika matashin shine mamallakin fitaccen shafin nan na Mujallar Zauren Marubuta da ke wallafa abubuwan da suka shafi marubuta ko 'yan fim dama sauran al'umma bakiɗaya a dandalin Facebook.Wakillin Manhaja a Katsina ya tattauna da Zaidu Ibrahim Barmo, a kan abubuwan da suka shafi aikace aikacensa, alaƙarsa da marubuta, shawara ga matasa, ƙalubalen da…
Read More
Har yanzu akwai marubutan da ba su rungumi sauyin da zamani ya kawo ba – Haiman Raees 

Har yanzu akwai marubutan da ba su rungumi sauyin da zamani ya kawo ba – Haiman Raees 

Ina da kyakkyawan zato game da adabin Hausa a nan gaba Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Jamilu Abdulrahman, wanda aka fi sani da Haiman Raees ba baƙo ba ne a tsakanin marubutan onlayin, musamman ma masu hulɗa da mahajojin kamfanin Bakandamiya Hikaya, inda bayan kasancewarsa marubuci kuma manazarci, harwayau shi ne yake jagorantar ɓangaren Bakandamiya Reading Club (BRC) sashin da ke kula da ilimantar da marubuta da inganta alaƙarsu da masu karatu. Haiman, wanda masanin harshen Indiyanci ne da Turanci, ya yi rubuce-rubuce a ɓangarorin adabi daban-daban. Bayan kasancewarsa marubucin waƙoƙin Hausa da Turanci, yana kuma nazari kan fasahohin waƙoƙin Indiya,…
Read More