Adabi

Yaƙin Tabuka da hikimar adabin baka

Yaƙin Tabuka da hikimar adabin baka

Daga SHEHU SANI LERE Yaƙin Tabuka, yaƙi ne da ba a kai ga yin sa ba, amma hikimar baka, ta sanya wani makaho a Arewacin Nijeriya (Na mance sunansa) tsaya wa ya shirya karatu cikin sigar waƙe da kalmomi majeranta masu bibiyar juna masu daɗin ji da saurare ga duk wanda a ke rera wa a gabansa. waƙar ta shahara a Ƙasar Hausa, ta yadda har kasa-kasan karatun a ke saida wa, a riqa saurara ana girgiza kai wasu na zibda hawaye. Haziƙin ya fi mai da hankali wajen fito da sadaukantakar Imamu Ali a cikin waƙen, ta yadda ya…
Read More
Darajojin Ahlul Baiti a cikin hadisai

Darajojin Ahlul Baiti a cikin hadisai

Daga MUHAMMED BALA GARBA Akwai Hadisai da dama da suka yi magana a kan martabobi da darajojin Ahlul Baiti. Za mu takaita kan wasu hadissai ingantattu guda bakwai (7). Amma bari mu soma da waɗannan guda biyu waɗanda suke bayyana fifikon dangin Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) baki ɗaya akan sauran mutane. Tirmizi ya rawaito falalar Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) cewa: Abbas (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: “Na ce wa Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), Ƙuraishawa sun zauna suna bitar tarihin gidansu. Sai suka kwatantaka da muruccin kan dutse. Sai Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Da Allah ya…
Read More
Akwai ƙalubale ga marubutan da suka dogara da rubutu kawai – Safna Jawabi

Akwai ƙalubale ga marubutan da suka dogara da rubutu kawai – Safna Jawabi

"Sanadin ababen da ke ƙunshe a zuciyata na fara rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata marubuta sun daɗe suna ba da gagarumar gudunmawa a vangaren cigaban adabi da harkokin rayuwa, saboda burin su na ganin sun kawo gyara a cikin al'umma da irin damar da suke da ita. Safna Aliyu Jawabi wata fitacciyar marubuciyar yanar gizo ce, daga Jihar Neja, wacce ta yi suna wajen fitar da littattafai da ke cike da darussa masu muhimmanci. A zantawarta da wakilin Manhaja a Jos, Safna ta shaida masa cewa, burinta na amfani da muryarta wajen kawo sauyi a rayuwar al'umma shi ya…
Read More
Rubutu mai inganci ne tushen cigaban marubuci – Yusuf Gumel

Rubutu mai inganci ne tushen cigaban marubuci – Yusuf Gumel

"Adabi ba zai taɓa mutuwa ba har sai an wayi gari babu wanda ya rage a duniya" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani salo da ya bambanta marubuta maza da mata, shi ne batutuwan da kowanne ɓangare ya fi mayar da hankali a kansa don faɗakar da al'umma. A yayin da a ɗaya vangaren akasarin marubuta mata ke rubutu kan batutuwan da suka shafi zamantakewar aure da rayuwa, maza sun fi baje basirarsu ne ta ɓangaren jarumta da almara ko abubuwa masu tsoratarwa, da kuma a wani batutuwan da suka shafi sarauta da siyasa. Ko da yake kowanne daga cikin waɗannan…
Read More
Shekaru shida na kwashe Ina ƙirƙirar baƙaƙe da lambobin Hausa – Sadar Musa

Shekaru shida na kwashe Ina ƙirƙirar baƙaƙe da lambobin Hausa – Sadar Musa

"Hausa harshe ne dake da rinjayen masu amfani da shi a Afrika" Daga AISHA ASAS a Abuja Idan ana zancen baiwa ta rubutu, ba na jin a faɗin Nijeriya akwai inda ya kai Arewa yawaitar marubuta da za a iya bugar ƙirji a kira su da gwanaye. Wataƙila namijin ƙoƙarin da suke yi ne ya haifar da wanzuwa da kuma raya yaren Hausa ga masu tasowa duk da irin horo da ruɗin da yaren Ingilishi ke yi a ƙwaƙwalensu. Cikin irin wannan ƙoƙari, aka samu wani matashi da ya yi kishin ƙirƙirar baƙaƙe da kuma lambobi da malam bahaushe zai buge ƙirji…
Read More
A sanadin rubutu na auri matata – Abu Hisham

A sanadin rubutu na auri matata – Abu Hisham

"Ana cin mutuncin adabi da rashin bin ƙa'idojin rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Akwai wasu mutane da Allah ya yi wa baiwa da kwarjini a rayuwar su, saboda tsarkin zuciyar su, kyakkyawan tunani da kuma ma dai wani sirrin da shi kaɗai ya bar wa kansa sani. Irin waɗannan mutane ko yaya suka nemi voye kansu ba sa vata ko da a cikin dubban jama'a, sai wani abu ya fitar da hasken su. Ana samun irin su a cikin kowacce al'umma cikin su kuwa har da marubuta, fitilun al'umma. Sunan Mukhtar Musa ƙarami da ake yi wa laƙabi da Abu…
Read More
Dalilan da suka sa na bugawa marubutan online littafi – Jibrin A. Rano

Dalilan da suka sa na bugawa marubutan online littafi – Jibrin A. Rano

"Daga manazarci ake zama marubuci " Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kawo yanzu kusan duk wani marubucin yanar gizo ko na online yana da labarin vullar wani mataimaki mai kishin cigaban adabi da rayuwar marubuta, wanda ya fito da wani tsari na tallafa wa marubutan online, ta hanyar buga musu littafin su na farko, don su ma su shiga sahun marubuta masu buga littafi. A cewarsa, burin kowanne mai rubutu ne a kira shi da marubuci, don haka bai dace a riƙa kallon waɗanda ke rubutu ta yanar gizo a matsayin ba cikakkun marubuta ba. A saboda haka ne ya ke…
Read More
Tarin kura-kurai a littafin ‘Halayyar Zamani’

Tarin kura-kurai a littafin ‘Halayyar Zamani’

Daga SANI AHMAD GIWA Littafin 'Halayyar Zamani' ɗaya ne daga cikin jerin littafan Adabin Kasuwar Kano, mai ɗauke da shafuka 148, wanda suka haɗu suka ja zaren labarin. Fa'iza S. Muhammad ce ta ƙaga labarin, inda maɗaba'ar Megacraft wadda ba a bayyana adireshinta ba ita ta wallafa shi, farashin da ake fansar shi a kasuwar littafai Naira 300 ne kacal. Bayan fansar wannan littafin a kasuwa, abin da zai biyo baya kuwa ai sharhin bayan karatu ne, a yunƙurin ya Allah ko dai yabo ko suka mai ma’ana a kan yadda manazarci ya ga littafin, ya kuma kalle shi, ko…
Read More
Tarihin Nana Faɗima ‘yar Manzon (3)

Tarihin Nana Faɗima ‘yar Manzon (3)

Daga MOHAMMED BALA GARBA, MAIDUGURI Haƙƙoƙin Ahlul Baiti a Kan Al’umar Musulmai Iyalan gidan Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) suna da waɗansu haƙƙoƙi guda Uku (3) waɗanda suka zama wajibi a kan kowane Musulmi. Ga su kamar haka: Ƙauna da Girmamawa: Iyalan gidan Manzo suna da wananan matsayi a cikin al’umma, dake wajabta a kaunace su da girmama su fiye da kowa. Abubuwan da muka ambata a baya ma sun isa hujja a kan wannan. Ba sai mun nemi kafa wata sabuwar hujja ba. Yi musu salati tare da mai gidansu: Yi wa Ahlul Baiti Salati tare da Manzon Allah…
Read More
Yadda Gasar Hikayata ta bana ta bambanta da saura

Yadda Gasar Hikayata ta bana ta bambanta da saura

*Abu mafi burgewa da mutumta rubutu game da gasar Hikayata shi ne kyautar da ake bayarwa - Amira Souley *Rubutu ba abu ne mai sauƙi ba, don haka ya kamata marubuta su dangwali arziƙin rubutu - Hassana Ɗanlarabawa *Hikayata dama ce ga mata na bayyana abinda ke ci masu tuwo a ƙwarya - Maryam Muhammad Sani Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Za a daɗe ba a manta da gasar 2022 ta gajerun labarai na Hikayata da Sashin Hausa na BBC Hausa ke shiryawa marubuta mata daga faɗin Afirka duk shekara ba, musamman ma dai ga gwarazan matan da suka samu nasara…
Read More