02
Mar
"Marubuci hantsi ne leƙa gidan kowa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Akwai kyakyawar alaƙa da zumunci mai ƙarfi tsakanin marubutan Nijar da Nijeriya kamar yadda marubuciya Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ta tabbatar a zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, inda ta bayyana sirrin nasarar da ake ganin marubutan Nijar na samu a shekarun baya bayan nan, musamman a gasar Hikayata ta BBC Hausa. A shekarar 2021 Nana Aicha ta zo mataki na biyu, yayin da a 2022 kuma Amira Souleymane ta samu nasara a mataki na farko. Abin arashin kuma shi ne dukkan su sun fito ne daga gari ɗaya wato Jihar…