07
May
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Hauwa Salisu, da ake yi wa laƙabi da Haupha, marubuciya ce daga Jihar Kaduna, yayin da ta fara aikin wani littafin ta mai suna 'Da Aurena' ba ta taɓa tunanin rubutun zai iya fuskantar tangarɗa ba, ganin irin yadda masu karatu suka karɓi littafin, saboda da salo na jan hankali da ta yi amfani da shi. Kwatsam, ran nan sai wata marubuciya daga ƙungiyar su ta Kainuwa ta sanar da ita cewa ana ɗora labarin ta a wani zaure da ke manhajar Facebook, amma ba tare da sunan littafin ba kuma ba da irin bangon da…
