10
Jul
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshen Babban Taron ƙungiyar Arewa Media Writers Association, da ta gudanar a garin Kaduna, an shawarci gwamnonin Arewa su kaucewa zubar da darajar sarautun gargajiya, saboda bambancin ra'ayin siyasa abin da ƙungiyar ke ganin rashin kishin Arewa ne ke haifar da haka. Ƙungiyar ta bayyana haka ne cikin takardar jawabin bayan taron da ta yi da shugabannin ƙungiyar a matakin ƙasa da jihohi, ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa Kwamred Haidar Hasheem Kano, inda ta fitar da wasu muhimman ƙudirori goma sha ɗaya. Ƙungiyar ta yi kakkausan suka ga abin da ta ce, wasa…
