Adabi

Ina son rubutuna ya zama silar sauyin rayuwar wasu – Safiyya Mukhtar Garba

Ina son rubutuna ya zama silar sauyin rayuwar wasu – Safiyya Mukhtar Garba

"Satar fasaha ce babba matsalar marubuta" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Safiyya Mukhtar Garba na daga cikin matasan da suke ƙoƙarin tasowa a tsakanin marubutan adabi. Ta fito ne daga Jihar Kano a Ƙaramar Hukumar Gwale. Tun Safiyya na ƴar shekara 13 ta fara nuna sha'awarta ga karatun littattafan Hausa, har ita ma ta kai ga tunanin fara ƙirƙirar nata labarin, sakamakon yadda ta fahimci cewa marubuta suna ba da gudunmawa ne ga gyaran al'umma ta hanyar rubuce-rubuce na hannunka mai sanda da nuni cikin nishaɗi. A tattaunawarta da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa burinta na…
Read More
Masarautar Burumawa (1)

Masarautar Burumawa (1)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau Manhaja za ta duba irin gwagwarmayar da ’ya’yan kabilar Burumawa suka yi wajen kafa masarautarsu a Jihar Filato. Burumawa, ƙabila ce wacce ta fi yawa a Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato, yawanta ya kai kashi 80 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Haka kuma ana samun su a Ƙaramar Hukumar Wase, inda a can yawansu ya kai kashi 40 cikin 100 na jama’ar ƙaramar hukumar. Sannan ana samun su a garuruwan qananan hukumomin Lantang da Shendem da Kua’an-Pan da sauransu a Jihar Filato da wasu yankunan Tsakiyar Nijeriya kamar Wukari a Jihar…
Read More
Nazarin Waƙar ‘Fatima Mai Zogale’

Nazarin Waƙar ‘Fatima Mai Zogale’

Daga ABBA ILIYASU IBRAHIM TSANYAWA Mawaƙi: Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu RararaMai Nazari: Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa. B.A (BUK) Gabatarwa: Waƙar 'Fatima Mai Zogale' da ta ja hankali a Arewacin Najeriya yanzu kuma ta samu shiga fagen nazari, inda wani marubuci kuma mai nazarin adabin baka Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa ya feɗe waƙar.Kwarjini da karɓuwa da kuma daɗin waƙar da salonta ake ganin ya ja hankalin mutane musamman matasa (maza da mata) da dattawa da sauran masu sha'awar harkokin adabin Hausa wajen tofa albarkacin bakinsu a kan waƙar, a daidai lokacin da ake cikin yanayin zaman tsadar rayuwa a ƙasar tare…
Read More
Ni ban ɗauki rubutun batsa a matsayin matsala ba – Mukhtar Yakubu

Ni ban ɗauki rubutun batsa a matsayin matsala ba – Mukhtar Yakubu

"Rubutu abu ɗaya ne, abin da za a rubuta ne ke bambanta su" Daga AISHA ASAS A wannan karon dai shafin adabi ɗan gida ya ɗauko maku, domin mun tattauna ne da ɗaya daga cikin daɗaɗɗun wakilan Manhaja, kuma marubuci da ya rubuta littafan hikaya da kuma na addinin Musulunci. A tattaunawar mai karatu zai ji yadda ɗan jaridar ya rikiɗe zuwa marubucin ƙagaggun labarai da kuma dangantakar da ke tsakanin aikin jarida da rubutun labari.Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Mukhtar Yakubu; MANHAJA: Duk da kai ba baƙo ba ne a Manhaja za mu so jin tarihin…
Read More
Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka. Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifakin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo. An yi imanin an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya yi ƙaurin…
Read More
Kafa makarantun boko na farko a Ƙasar Hausa

Kafa makarantun boko na farko a Ƙasar Hausa

Daga SADIQ TUKUR GWARZO Kafin a gabatar da ilimin boko a Jihohin Arewa, sai da Gwamna Lugga ya sa aka yi bincike aka gano yawan makarantun allo da ake da su, da yawan almajiransu. A cikin wani kintaci-faɗi an gano cewa a farkon ƙarni na ashirin, akwai makarantun allo guda 25,009 masu yawan ɗalibai 218,618 a garuruwan jihar Arewa. Ganin ƙarfin ilimin addininin Musulunci, sai Gwamna Lugga ya ga cewa ba daidai ba ne a gabatar musu da ilimin boko kamar yadda ake tafiyar da shi a Ingila. Mun dai riga mun sani tun wajen shekarar 1900 aka buɗe makarantun…
Read More
Ana yi wa harkar rubutu shiga shantun ƙadangare – Abou Othaymeen

Ana yi wa harkar rubutu shiga shantun ƙadangare – Abou Othaymeen

"Ina fatan na narka ruwan gwalagwalan hikimomin da aka yi mini baiwar sa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Malam Nura Isma'il, wanda aka fi sani da Abou Othaymeen, ba voyayye ba ne a tsakanin marubutan adabi na Hausa da Turanci, har ma da Larabci. Ya daɗe yana ba da gudunmawa a ɓangaren adabin zube da rubutattun waƙoƙi. Sannan kuma har wa yau hafizi ne na Alƙur'ani Mai Girma, kuma malamin makaranta. Shi ne ya jagoranci tilawar haddar Alƙur'ani Mai Girma da marubuta suka gudanar a zauren marubuta na manhajar WhatsApp. A tattaunawar sa da Abba Abubakar Yakubu, Malam Nura, ya bayyana…
Read More
Tasgaron zuwan Turawa Ƙasar Hausa

Tasgaron zuwan Turawa Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Duk da irin alfanu da muka zayyana waɗanda suka samu a Ƙasar Hausa sakamakon zuwan Bature, ba kuma za a rasa tasgaro, cigaban mai haƙar rijiya, da kuma koma baya waɗanda zuwan Turawa ya haifar ba. Tabbataccen abu ne a tsarin rayuwa, cewa, duk lokacin da aka samu sauyi ko cuɗanya da wasu baƙin jama’a, waɗanda tasirinsu ya kai ga wata jama’ar ta sauya salon yadda take gudanar da rayuwarta, babu makawa, sai an samu abubuwan da za su saɓa da abin da yake karɓaɓɓe a tafarkin rayuwar waɗannan jama’a da aka zo aka taras. Zuwan…
Read More
Yana da kyau marubuta su ƙirƙiro da hanyar mayar da rubutunsu kan sauti – Farfesa Sufyan Wase

Yana da kyau marubuta su ƙirƙiro da hanyar mayar da rubutunsu kan sauti – Farfesa Sufyan Wase

"Ya kamata marubuta su riƙa tafiya da zamani" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuta sun kasu kashi daban-daban. Akwai marubutan labaran hikaya, akwai marubutan tarihi, akwai marubutan faɗakarwa, akwai kuma na ilimi. Sufyanu Adamu Yakubu mai laƙabi da Farfesan Marubuta, marubucin kalmomin hikima ne da faɗakarwa, musamman abin da ya shafi zamantakewa da tarbiyya. Kasancewarsa malamin makaranta, hakan ya taimaka masa wajen yin rubuce-rubuce da suka shafi ilimi da cigaban rayuwa. A zantawarsa da Abba Abubakar Yakubu, Farfesan ya bayyana burinsa na zama cikakken Farfesa na gaske, kuma mawallafin littattafan kimiyya. A yi karatu lafiya. MANHAJA: Zan so ka fara gabatar…
Read More
Marubuta sun yi rawar gani cikin Ramadan – Queen Nasmah

Marubuta sun yi rawar gani cikin Ramadan – Queen Nasmah

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A cigaba da kawo muku tattaunawar da muka yi da marubuta da ƙungiyoyi game da ayyukan da suka gudanar cikin Ramadan, ƙarƙashin ƙungiyoyi da jagorori daban-daban. A wannan makon muna ɗauke ne da tattaunawar da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi da wata marubuciya Asma'u Lawal Liman, wacce aka fi sani da Queen Nasmah, shugabar ƙungiyar Moonlight Writers Association. A zantawar da suka yi Nasmah ta bayyana irin shirye-shiryen da suka gabatar da kuma ayyukan da suke yi na jinqƙai da taimakawa mabuƙata, a lokacin azumi da bayansa. MANHAJA: Mu fara da sanin wacce…
Read More