Adabi

Alfanun zuwan Turawa ƙasar Hausa

Alfanun zuwan Turawa ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wannan cigaba ne daga rubutun makon da ya gabata. Duk da cewa, Bature ya zo ya samu Bahaushe da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauransu. Amma duk da irin wannan cigaba da Bahaushe yake da shi kafin zuwan Turawa, an samu ƙarin cigaba a fannonin da dama sakamakon zuwan nasu. Wannan cigaban kuwa ya sauya yanayin yadda Bahaushe yake gudanar da harkokinsa na rayuwa kusan baki ɗaya sai dai ‘yan abubuwan da ba za a rasa ba. Idan muka kalli yanayin yadda Bahaushe yake gudanar da harkokinsa na…
Read More
Ya kamata marubuta su riƙa taimakawa mabuƙata – Nimcyluv

Ya kamata marubuta su riƙa taimakawa mabuƙata – Nimcyluv

"Na ciyar da mabuƙata fiye da ɗari cikin Ramadan" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Tun da watan Ramadan ya kama a wannan shekara, marubutan adabi maza da mata suka shiga cikin hidimar kyautata addininsu da kusancinsu da Allah, ban da shirye-shirye da suke gabatarwa a zaurukansu na Facebook da whatsapp, wasu kuwa har ƙungiyoyi ne da su da suke tallafa wa mabuƙata da ciyar da su abincin buɗe-baki. Na'ima Suleiman Sarauta na daga cikin marubutan da suke gudanar da irin wannan aikin neman lada na ciyarwa da taimakon marayu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Nimcyluv kamar yadda…
Read More
Anka ya zama shugaban ƙungiyar Hausa ta BUK

Anka ya zama shugaban ƙungiyar Hausa ta BUK

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Fitaccen marubucin littattafan Hausa da finafinan Kannywood, Malam Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi sani da ANKA ya zama shugaban ƙungiyar Hausa ta Jami'ar Bayero da ke Kano, a wani zaɓe da ƙungiyar ta gudanar ranar Jumma'ar da ta gabata 22 ga watan Maris, 2024 a zangon karatu na 2022/2023. Marubucin wanda yake ɗalibta a Sashin Nazarin Harsunan Najeriya, inda yake karatun digirinsa na farko a fannin Harshen Hausa, ya zama shugaban ƙungiyar ne bayan zaven da aka yi masa tare da wasu masu dafa masa su goma sha ɗaya. Da suka haɗa da shi, Kabiru…
Read More
Ko kun san tarihin fadar Aso Rock Villa?

Ko kun san tarihin fadar Aso Rock Villa?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fadar Gwamnatin Tarayya wadda ake kira State House a Turance. Wannan fada, ayari ne na ofisoshi da suka haɗa da Fadar Shugaban Ƙasa wadda ake kira Presidential Villa a Turance; ofishin mataimakin shugaban ƙasa, da sauransu. Haka nan kuma a cikin fadar ta shugaban ƙasa akwai ma’aikatan da suke gudanar da ayyukan da suka shafi ayyukan gudanarwa, tsare-tsare bisa ƙa’ida, harkar tsaron lafiyar shugaban ƙasa da fadar tasa da kuma harkokin yaɗa labarai, waɗanda dukkan su suke ƙarƙashin kulawar shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Tarayya, wato Chief of Staff kenan, muƙamin da a yanzu haka (2024), Femi…
Read More
Rashin haɗin kai ne ke hana tasirin marubutan Jihar Sakkwato – Zarah BB

Rashin haɗin kai ne ke hana tasirin marubutan Jihar Sakkwato – Zarah BB

"Rubutu madubi ne da ke haska gobe" Daga AISHA ASAS Jihar Sakkwato na ɗaya daga cikin jihohin da ke ɗauke da kwararrun marubuta duk da cewa ba kasafai ake sanin su ba, wataƙila hakan ba ya rasa nasaba da daidaitacciyar Hausa da suke amfani da ita, wadda ke hana a gane su da Hausa irin ta Sakwatawa, har sai dai idan su ne suka faɗa. A yau shafin adabi ya ɗauko ma ku ɗaya daga cikin jajirtattun marubuta da suka fito daga Birnin Shehu, Fatima Bello Bala, wacce aka fi sani da Zarah BB. Matashiyar marubuciya ce da ke bada…
Read More
Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari'a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane. Lokacin da Ahmed Baba ya rayu: An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu…
Read More
Rubutu ya sauya min rayuwata da duniyata – Ramlat Manga Maidambu

Rubutu ya sauya min rayuwata da duniyata – Ramlat Manga Maidambu

"Na sha wahalar rubuta littafina na farko" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ramlat Abdulrahman Manga, wacce aka fi sani da Maidambu, na daga cikin jajirtattun marubuta onlayin da aka sha gwagwarmaya da su a duniyar marubuta, tun ba a san ko ita wacce ce ba. Ta yi rubuce rubuce da dama, waɗanda suka samu karvuwa a wajen jama'a har kuma ita ma ta yarda cewa ta samu alheri sosai. Tana daga cikin marubutan adabi da suka fito daga Jihar Bauci kuma take bai wa mara ɗa kunya wajen ɗaga sunan jihar a harkar batun rubuce-rubucen Hausa. A zantawarta da Abba Abubakar…
Read More
An karrama marubuci Abba Abubakar Yakubu

An karrama marubuci Abba Abubakar Yakubu

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos Fitaccen marubucin nan kuma jarumin finafinan Kannywood, Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ya taɓa faɗa cewa, 'Duk wani abu mai kyau da ka ke yi duniya tana gani, kuma wata rana za ka samu sakamakonsa.' Wannan bayani nasa ne ya fito a fili jama'a suka shaida, a ƙarshen makon da ya gabata, inda wata cibiya mai koyar da ilimin fasahar sadarwa da kula da adana littattafai, wato Information and Library Science, mai suna Majema College of Advanced Studies Jos ta karrama marubuci kuma ɗan jarida, Abba Abubakar Yakubu, sakamakon jajircewa da gudunmawar da yake…
Read More
Yadda marubutan adabi suka yi bikin Ranar Marubuta ta 2024

Yadda marubutan adabi suka yi bikin Ranar Marubuta ta 2024

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ana gudanar da bikin Ranar Marubuta ta Duniya ne a ranar 3 ga watan Maris na kowacce shekara, domin ƙara zaburar da marubuta a ko'ina a duniya game da gudunmawar da suke bayarwa wajen faɗakarwa da ilimantar da jama'a da suke yi, musamman matasa da ɗaliban ilimi. Tun a shekarar 1986 aka fara bikin ranar a faɗin duniya, bayan shawarwarin da ƙungiyoyin marubuta da mawaqƙa daban-daban suka riƙa bayarwa don ganin an ware wata rana guda da za a riƙa tattauna abubuwan da suka shafi harkar rubutu da basirar ƙirƙira. Sau da dama jama'a sun fi…
Read More
Makaɗin Hausa: Marigayi Alhaji Sa’idu Mai Daji Sabon-Birni

Makaɗin Hausa: Marigayi Alhaji Sa’idu Mai Daji Sabon-Birni

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haifi Alhaji Sa’idu Mai Daji a garin Tara ta sarkin Kwanni, ita kuma Tara tana bin Sabon-Birni ta sarkin Gobir, jihar Sakkwato. Sannan mahaifinsa shi ne Mainasara. Ya kiyasta cewa yana da shekara arba’in da biyar (45), watau ke nan an haife shi a wajejen 1938. Dalilin kiransa Maidaji shi ne, a lokacin rayuwar mahaifinsa suna zaune ne a tsohon garin Tara. Sai wata rigima da faɗace-faɗace ta haddasu tsakanin mutanen Tarar, sai aka yi ta tashi ana barin garin, bayan kuwa har sun yi shuka. Mahaifinsa Mainasara, ya ce shi kam ba zai bar…
Read More