07
Mar
"Manazarcin Hausa na samun tagomashi mai tsoka a harkar fashin baƙi ko tambihi" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mubarak Idris Jikamshi, matashin marubuci ne daga Jihar Katsina, duk da kasancewar bai fitar da wasu littattafai masu yawa ba, amma yana da gajerun labarai da dama da ya yi, wasu ma har ya shiga gasannin marubuta da su, a mataki daban-daban. Wani abu da ya bambanta Mubarak da sauran marubuta shi ne kishin da yake da shi a nazarin ilimin harshen Hausa da kula da kiyaye ƙa'idojin rubutu, don yanzu haka yana matakin fara digirinsa na biyu ne a harshen Hausa. Bayan…
