30
Jan
Tare da MAHDI M. MUHAMMAD Blueprint Manhaja ta yi nazari tare da tattaro bayanai dangane da labarin rikicin Maitatsine. Makasudin rikicin Maitatsine ya faru ne a ranar 11/12/1980, wato kusan a ce ya faru ne a unguwar Malafa. Malafa unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce ta ke da mashahuran mutane masu arziki, malamai da ’yan kasuwa da sauransu, misali a bangaren masu arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza. A bangaren malamai kuma, akwai irinsu Malam Umar Sani Fagge, da Malam Haido da su Malam Muktar Atamma, wanda duk a yankin…
