Adabi

Marigayi Haruna Kundila: Mutumin da ya fi kowa arziki a Kano kafin zuwan Turawa

Marigayi Haruna Kundila: Mutumin da ya fi kowa arziki a Kano kafin zuwan Turawa

Daga IBRAHIM HAMISU A cikin waƙar Marigayi Malam Sa'adu Zungur (1915 - 1958) mai taken Arewa Mulukiya ko Jamhuriya, ya ce, "Ya Sarki Alhaji Bayero, Ga ’yan birni da Kanawiya. "Tun Bagauda na saran Kano, Suka fara fataucin dukiya." A tarihi, jihar Kano ta kasance cibiya ta siye da sayarwa, ma'ana kasuwanci. Tarihi ya kuma bayyana cewa jihar ta haifi manyan mutane masu ƙarfin arziki da dama waɗanda suka yi shuhura da kafa tarihin da ba za a manta da su ba. Ba a iya wannan qarnin ba ne kawai jihar Kano ta samu manyan masu arziki ba, Allah ya…
Read More
Shigowar gwamnati da ‘yan kasuwa zai kawo bunƙasar rubutun adabi – Shamsiyya Manga

Shigowar gwamnati da ‘yan kasuwa zai kawo bunƙasar rubutun adabi – Shamsiyya Manga

"Marubuta ku tsaftace alƙalaminku ko don goben ku ta yi kyau" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Cigaba da tumbatsar da ake samu ta marubuta a kafafen sadarwa na zamani, bai hana waɗanda suka yi fice kuma suka goge da sha'anin rubutu, samun nasarori da ɗaukaka ba. Wasu marubuta na ganin yawan masu rubutu a onlayin ba ya hana su samun masoya da masu bibiyar littattafansu, duk kuwa da cewa da ake yi, idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Shamsiyya Usman Manga, na daga cikin matasan marubuta da tauraruwarsu ke haskawa. Kuma bayan kasancewarta marubuciya har wa yau Ungozoma…
Read More
Tarihin rayuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu

Tarihin rayuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haife shi a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952 cikin birnin Legas. Bola Tinubu Musulmi ne kuma ya halarci makarantar firamare mai suna St. John's Primary School, da ke Aroloya da ke birnin Legas, sai sakandiren Children's Home School da ke Ibadan. Tinubu ya samu tafiya ƙasar Amurka domin ƙaro karatu a shekarar 1975, inda ya fara karatu a Kwalejin Richard J. Daley College da ke Chicago, Illinois kafin daga bisani ya koma jami'ar jihar Chicago mai suna Chicago State University. Ya samu kammala digirinsa a shekarar 1979 daga wannan jami'ar inda ya…
Read More
Mansa Musa: Mutum mafi arziki a tarihin duniya

Mansa Musa: Mutum mafi arziki a tarihin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sarkin daular Mali, Mansa Musa, wanda a wasu lokutan akan kira shi da ‘Kanku Musa’ ya kasance mutum mafi ƙarfin arziki da aka taɓa samu a duniya. Wadatarsa ta ba shi damar mayar da Timbuktu cikin birni mai ban mamaki. Ya yi sarauta tsakanin shekarar 1313 zuwa 1337. Mansa Musa shi ne Sarki na goma a jerin sarakunan masarautar Mali, kuma yana da arzikin da a yanzu darajarta ta haura dala biliyan 400. An haifi Kanku Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Koda yake ana yawan kiran shi Kankan Musa, amma ainihin sunansa 'Kanku'.…
Read More
Mahaifiyar marubuci Ayuba M. Ɗanzaki ta kwanta dama

Mahaifiyar marubuci Ayuba M. Ɗanzaki ta kwanta dama

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Ayuba Muhammad Ɗanzaki dai fitaccen marubucin hikaya ne da yake yin rubutunsa cikin harshen Hausa na zube da kuma rubutacciyar waƙa musamman ta yabo ga Fiyayyan Halitta (S.A.W.). Ya wallafa littafai da dama, waɗanda suka haɗa da 'Shingen Ƙauna, Adawar So, Rayuwar Bilkisu, Fadar So, Kurman Hisabi' da dai sauransu. Mahaifiyar ta marubuci Ayuba Muhammad Ɗanzaki dai wato Hajiya Salamatu Garba Zakirai, wadda aka fi sani da Hajiya Talatuwa Ɗanzaki ta rasu ne ranar da ta gabata daidai da 4/5/2023, da ƙarfe Sha Biyu na dare (12:00AM). Cikin tattaunawar da wakilinmu ya yi da…
Read More
Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (II)

Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau za mu cigaba da kawo tarihin hawan sallah na masarauto daban-daban daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. Masarautar Gwandu: Hawan Sallah a Masarautar Gwandu ya samo asali da daɗewa tun zamanin sarakuna kuma an fara ne bayan Jihadi kamar yadda Alhaji Ibrahim Baisat, Galadiman Gwandu ya shaida. Yayin hawan idi da ƙaramar sallah, uwayen ƙasa na ƙasar Gwandu 15 duk suna zuwa da dawakai 30 ko 40 wasu ma 50. A cewarsa, ana gudanar da hawan farko bayan sallar idi. "Idan aka (idar) da idi, ana fara kiɗi, lokacin kakaki su…
Read More
Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (I)

Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (I)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hawan Sallah wata al'ada ce da ta daɗe a tarihin Masarautun Ƙasar Hausa. Masarautar Kano: A wannan masarauta, akwai hawan sallah da ake yi duk shekara a lokacin ƙarama da kuma babbar sallah. Bayanai na cewa Muhammadu Rumfa ne ya assasa tsarin hawan sallah a Kano. Daga cikinsu akwai Hawan ranar sallah da Hawan Nasarawa da Hawan Ɗorayi da Hawan Daushe da Hawan Fanisau. Sai dai daga cikin waɗannan haye-haye da ake yi a Masarautar Kano, guda biyu ne suka fi jan hankali. Hawan Nassarawa: Yayin wannan hawan, sarki na zuwa gidansa da ke Nassarawa daga…
Read More
Sharhin littafin ‘Jiki Magayi’

Sharhin littafin ‘Jiki Magayi’

Daga KABIRU YUSUF FAGGE (ANKA) Sunan littafi: Jiki MagayiMarubuta: John Tafida Umaru Zariya da Rupert EastShekarar Bugawa: 1995Maɗaba’a: Northern Nigeria Publishing Company (NNPC)Bugawa: Ahmad Bello University Press, Samaru, ZariaYawan Shafuka: 52Mai Nazari: Kabiru Yusuf Fagge (Anka) Jiki Magayi labari ne na wani ƙasurgumin kuma shahararren attajiri mai suna Mallam Shaihu mazaunin cikin birnin Galma. Saboda yawan kuɗin Mallam Shaihu ba inda sunan shi bai kai ba (shafi na 1). Kai hatta shi kan shi Mallam Shaihu bai san yawan dukiyarsa ba (shafi na 2). Sai dai kash! Duk da tarin dukiyar Mallam Shaihu, Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba,…
Read More
Alfanun tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen duniya

Alfanun tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A baya mun duba tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen, da dalilan da suka kai su in ma ta hanyar fatauci ne, ko cinkayyar bayi. Baya ga haka mun ga ire-iren ƙasashen da suka je kamar Tiripoli da ke Libiya da Chadi, da Turai kamar kudancin Amurka da suka haɗa da Brazil da sauransu. A bisa kyakkyawan bincike da nazari, duk inda aka samu wata al’umma tana gudanar da harkokin rayuwarta to, nan ne take tafiyar da al’amuran rayuwarta da suka haɗa da al’adunta da amfani da harshenta wanda shi ne harshen adabi mai nuna irin azancinta…
Read More
Duk wanda ya buga littafi a wannan runtsi ba ƙaramin jarumi ba ne – Zubairu Balannaji

Duk wanda ya buga littafi a wannan runtsi ba ƙaramin jarumi ba ne – Zubairu Balannaji

"Ina jin takaicin tarin kura-kuran da ake yi a allunan talla" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Zubairu Balannaji ba boyayyen suna ba ne, musamman a tsakanin marubuta na Jihar Kano, inda yake rayuwa kuma yake baje irin tasa basirar da Allah Ya ba shi ta ƙirƙirar labari, da fitar da labarin da aka sawwala shi daga tunani zuwa ga rayuwa, ma'ana dai ya mayar da shi zuwa fim. Matashin marubucin littattafan adabi, marubucin wasan kwaikwayo, mai shiryawa da tsara finafinan Hausa, kuma a gefe guda ɗan kasuwa. A tattaunawar sa da ABBA ABUBAKAR YAKUBU fasihin marubucin ya bayyana irin gwagwarmayar da…
Read More