Marigayi Haruna Kundila: Mutumin da ya fi kowa arziki a Kano kafin zuwan Turawa

Daga IBRAHIM HAMISU

A cikin waƙar Marigayi Malam Sa’adu Zungur (1915 – 1958) mai taken Arewa Mulukiya ko Jamhuriya, ya ce, “Ya Sarki Alhaji Bayero, Ga ’yan birni da Kanawiya.

“Tun Bagauda na saran Kano, Suka fara fataucin dukiya.”

A tarihi, jihar Kano ta kasance cibiya ta siye da sayarwa, ma’ana kasuwanci. Tarihi ya kuma bayyana cewa jihar ta haifi manyan mutane masu ƙarfin arziki da dama waɗanda suka yi shuhura da kafa tarihin da ba za a manta da su ba.

Ba a iya wannan qarnin ba ne kawai jihar Kano ta samu manyan masu arziki ba, Allah ya albarkace ta da su a qarnika da suka gabata. Jihar ta yi manyan attajirai da dama kamar su Madugu Indo Adakawa, Muhammadu Ɗan Agigi, Madugu Ɗangomba, Umaru Sharubutu, Mai Kano Agogo, Alhasasan Ɗantata, Adamu Jakada, Muhammad Nagoda da wasu masu yawa ma da ba a ambata ba.

Marigayi Alhaji Haruna Kundila (1810 – 1901) ya shahara saboda ɗumbin arzikin da Allah ya ba shi a Kano, kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, lokacin mulkin Sarkin Kano Marigayi Alhaji Abdullahi Maje Kafofi da wanda ya maye gurbinsa, wato Sarki Bello Ibrahim Dabo.

Akwai wata sananniyar karin magana da ake danganta ta da shi da ake cewa, “Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila.” Hakan na nufin babu abin da Kundila ba zai iya siya ba, sai dai idan ba na siyarwa ba ne, saboda da tarin arziƙin da Allah ya yi masa.

An haifi Kundila a shekarar 1810 a unguwar Makwarari, birnin Kano.

Tarihin silar arzikinsa ya bayyana cewa: “Wata rana ya fito daga gidansa sai ya haɗu da Malam Sidi. Tarihi ya bayyana cewa Malam Sidi wani shahararren malamin addinin Muslunci ne mai matuƙar tsoron Allah da mutane da yawa suka yi imanin waliyyi ne. Da haɗuwar su sai Mallam Sidi ya roƙe shi kan ya taimaka ya nemo masa waɗanda za su yashe masa shaddar gidansa. Kundila ya ce to tare da tafiya neman masu yasar shadda.

Ya kewaya gari amma ya gaza samun waɗanda za su yi aikin. Hakan ya sanya ya yanke hukuncin yashe shaddar malamin da kansa. Da malamin ya dawo sai ya tambaye shi, shin ko ya samu mutanen da za su yi aikin? Cikin girmamawa ya amsa da faɗin ai mutanen sun zo har sun kammala aikin. Malaman ya kuma tambayar sa, “Nawa ya kamata a biya su ladan aikinsu?”

Bai kai ga amsawa ba sai wani mutumi da ya ga yadda Kundila yai aikin shi ɗaya yai wuf ya bayyana wa malamin cewa ai Kundila ɗin ne ya yi aikin da kansa.

Da malamin ya ji sai ya kaɗa kansa ya ce, “To, Insha Allahu, duk inda warin masan nan ya buga, Gabas da Yamma; Kudu da Arewa, sai ka yi suna, ka shahara, an san ka”.

Tarihi ya bayyana cewa, Haruna Kundila, wanda ya kasance mai cinikin bayi a wancan lokacin, ya yi mu’amala ta kasuwanci da masu ciniki da ke zuwa ƙasar Kano daga ƙasashen waje kamar Mali, Sudan, Libiya, Sanigal, Damagaram, Agadas, Garwa, Duwala, Bamyo, da Fallomi.

A lokacin da ludayinsa ke kan dawo, babu wani mai arziki a ƙasar Kano da ya kama qafarsa. Ya kasance mutum mai tarin dukiya, kuma yana da manyan gidaje a kowacce ƙofar shiga birnin Kano. An ce yana da bayi sama da dubu. A takaice, shi ne hamshaƙin ɗan kasuwan da ya zarce kowa a ƙarni na 19 a ƙasar Kano.

Dalilin da ya sa ake masa laƙabi da Kundila:

Tarihi ya bayyana cewa Haruna ya kasance yana da ƙanwa mai bin sa a haihuwa da ake kira da suna Binta. Bayan ta girma, wata rana ya je gida sai ya tarar da ƙanwar tasa a ɗakin mahaifiyarsu. Ya ce mata, “Taimaka Binta ki miqo min kundina.”

Da ta ji shi sai ta dinga maimaitawa, “Ina kundina? Ina kundin?” Tun daga wannan lokacin sunan Kundila ya bi shi har bayan rayuwarsa. Har zuwa yanzu wasu rukunin gidajen gwamnati a jihar Kano suna ɗauke da sunansa. Misali, Kundilar titin Zaria.

An ce a lokacin da Allah ya karvi ransa a 1901 (shekaru biyu kafin sojojin turawan mulkin mallaka su mamaye birnin Kano) Kano ta girgiza matuqa sakamakon rasa ɗaya daga cikin manyan attajiranta.

Yasir Kallah ne ya fassaro wannan tarihin daga shafin Northbook, wanda Jamilu Uba Adamu ya wallafa cikin Harshen Ingilishi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *