21
Jul
Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano An bayyana cewa yadda zaɓen ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa NAKSS reshen Jihar Kano cikin kwanciyar hankali da lumana abun farin ciki ne, kuma nasara ne ga ɗaliban Jihar kano da na Nijeriya baki ɗaya, kamar dai yadda mai ba gwamnan Kano Shawara kan Harkokin Ɗalibai Hon Ibrahim Ma'aji ya bayana bayan kammala zaɓen da kuma rantsar da shugabanin NAKSS a ranar Lahadi da ta gabata. Sai kuma yadda ɗaliban Kano da ke karatu a manyan makarantun kano da sasan ƙasar nan yanzu haka sun zaɓi kwamred Isyaku Ali Kanwa, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ɗalibai…
