Siyasa

Zanga-zanga: Lauyoyin Obi sun buƙaci Onanuga ya janye kalamansa ko ya fiskanci shari’a 

Zanga-zanga: Lauyoyin Obi sun buƙaci Onanuga ya janye kalamansa ko ya fiskanci shari’a 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi ya bai wa Mista Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, sa’o’i 72 da ya biya Naira biliyan 5 a matsayin diyya da kuma neman afuwarsa a cikin manyan jaridun ƙasa guda huɗu saboda ɓata suna da cin mutuncin Obi da suka ce ya yi,ko kuma ya fuskanci shari'a Obi ya buƙaci Mista Onanuga, ya janye zargin da ya yi masa na ƙage, tare da alaƙanta shi da zanga-zangar da aka shirya yi…
Read More
Waɗanda suka yi zanga-zanga a 2012 na son danne haƙƙin jama’a — Atiku

Waɗanda suka yi zanga-zanga a 2012 na son danne haƙƙin jama’a — Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta. Atiku ya bayyana yunƙurin da abun dariya, saboda waɗanda ke ƙoƙarin hana zanga-zangar su ne waɗanda suka yi wa tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zanga-zanga a shekarar 2012. Zanga-zangar, wadda matasa suka shirya, na da nufin jawo hankali kan ƙaruwar yunwa da wahala da ’yan ƙasa ke fuskanta. Masu shirya zanga-zangar sun ce za a shafe kwanaki 10 duba da halin matsi da ke ƙara ta’azzara, wanda suka ce…
Read More
Burin kyautata ci gaban al’ummar Fagge ya sa na amsa kiran tsayawa takara – Aliyu Sanata 

Burin kyautata ci gaban al’ummar Fagge ya sa na amsa kiran tsayawa takara – Aliyu Sanata 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗaya daga masu neman tsayawa takarar shugabancin Ƙaramar Hukumar Fagge a ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP, Hon. Aliyu Tijjani Inuwa da ake yi wa laƙabi da Sanata, ya ce sakamakon tafiyar su ta Kwankwasiyya an sha tiri-tiri shekara takwas har aka kai ga samun nasarar a zaɓe ba shi da niyyar yin wata takara sai da jama'a suka yi ta kiraye-kirayen ya fito takara. Ya ce  ganin al'umma sun nuna cancantarsa na ganin zai aikata abinda ya dace a ƙaramar hukumar Fagge domin shi tun babu gwamnati ko wani muƙami yake abinda masu muƙami a tsohuwar gwamnati…
Read More
Wike ba ɗan jam’iyyarmu ba ne,  cewar APC a Jihar Ribas

Wike ba ɗan jam’iyyarmu ba ne,  cewar APC a Jihar Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Talatar da ta gabata ne jam’iyyar All Progressiɓes Congress ta yi watsi da raɗe-raɗin da ake yi cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike na yin tasiri a kan hukuncin da jam’iyyar reshen jihar Ribas ta ɗauka. Jam’iyyar ta musanta raɗe-raɗin, inda ta ce tsohon gwamnan Ribas ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, kuma ba ya halartar duk wani taron su na siyasa. Da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja, Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC na Ribas, Cif Tony Okocha, ya bayyana cewa duk…
Read More
Gwamnan Kebbi ya rushe kantomomin ƙananan hukumomi

Gwamnan Kebbi ya rushe kantomomin ƙananan hukumomi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Kebbi Nasiru Idris ya rushe shugabannin riko na daukacin kananan hukumomi da ke Jihar. Sanarwar da Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu na jihar, Aliyu Hassan Kalgo ya fitar ta ce rushe kantomomin ya fara aiki ne nan take. Sanarwar da aka fitar a madadin kwamishinan ma’aikatar, ta umarci rusassun kantomomin sun mika ragamar gudanar da ofisoshinsu da daraktocin gudanarwar kananan hukumominsu. Gwamnan ya nada kantomin ne bayan karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar a watan Fabrairun shekarar 2023 da ta gabata. Rushe kanomomin ba zai rasa nasaba da da…
Read More
Zanga-zanga: Ka saurari koken ‘yan Nijeriya, Ndume ya shawarci Tinubu

Zanga-zanga: Ka saurari koken ‘yan Nijeriya, Ndume ya shawarci Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya saurari buƙatun 'yan Nijeriya waɗanda ke shirin yin zanga-zanga. Ndume ya yi wannan kiran ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TƁ a wani shirin sa mai taken Politics Today. Da aka tambaye shi ya yi tsokaci kan kiran da shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) Joe Ajaero ya yi wa shugaban ƙasar na ya tattauna da 'yan ƙasa, Ndume ya ce ya amince da wannan kira. Ya ce, “Na goyi bayan wannan…
Read More
Muna samun nasarar haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Jihar Kano – Hon Abdurrahman Salga

Muna samun nasarar haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Jihar Kano – Hon Abdurrahman Salga

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jigo a fafutukar samar da haɗin kai domin tafiya ɗaya a Jam'iyyar PDP wanda ya yi wa jam'iyyar takarar neman majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Dala a zaɓen 2023, Hon Abdurrahman M Salga da aka fi Sani da Mai Nasara ya bayyana cewa kullum ƙudurinsa a rayuwa shine ya ga  matasa sun sami abin yi duba da irin abubuwa da ke faruwa a Kano akwai ƙalubale. Ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a wajen taron yaye matasa da aka koyawa gyaran waya a ƙarƙashin Bash communication. Ya nuna cewa akwai zalunci irin…
Read More
APC ta kasa mamaye Kudu maso Gabas ne saboda yankin na yi wa ‘yan jam’iyyar kallon sun maida su saniyar-ware – Ganduje

APC ta kasa mamaye Kudu maso Gabas ne saboda yankin na yi wa ‘yan jam’iyyar kallon sun maida su saniyar-ware – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana irin ƙoƙarin da ya ce APC ke yi domin ƙwace sauran jihohin Kudu maso Gabas daga hannun jam’iyyun adawa. Ganduje ya ce APC ta kasa kama jihohin Enugu, Abiya da Anambra ne, saboda ‘yan yankin na yi wa shugabannin cikin APC kallon su na cikin waɗanda suka maida su saniyar-ware a siyasa da mulkin Nijeriya. Ganduje ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi wurin taron Majiɓinta Lamarin APC na Yankin Kudu maso Gabas, a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi. A Kudu maso Gabas dai jihohin…
Read More
Kashi biyar ne kacal na mata ke riƙe da muƙaman siyasa a Nijeriya — Shugabar mata ta APC

Kashi biyar ne kacal na mata ke riƙe da muƙaman siyasa a Nijeriya — Shugabar mata ta APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabar mata ta Jam’iyyar APC ta Ƙasa, Dakta Mary Idele Alile, ta ce kashi 5 cikin 100 ne kacal na mata a Nijeriya ke rikƙe da muƙaman siyasa. Dr Mary ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin bunƙasa damarmakin mata a riƙa damawa da su a siyasa, wanda aka yi shi a Sakkwato a ƙarshen mako. A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishinta, ta yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da ya ke yi na sauya yanayin ta hanyar baiwa mata muƙamai…
Read More
Ba a yi wa Tinubu katangar hana shi ganin mutane ba, APC ta yi wa Ndume martani

Ba a yi wa Tinubu katangar hana shi ganin mutane ba, APC ta yi wa Ndume martani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC ta yi abin da Bahaushe ke cewa ‘ka fi mai kora sosawa’, yayin da ta nuna jin ciwon zafafan kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. APC ta yi masa raddin cewa kasa samun damar ganawar da Ndume ya yi da Tinubu ba zai taɓa zama dalili ko hujjar cewa wasu sun kange shugaban ƙasar daga ganawa da ‘yan Nijeriya ba. Sakataren Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Feliɗ Morka ne ya yi wa Ndume wannan raddi, wanda ke ƙunshe cikin sanarwar da ya raba wa manema…
Read More