11
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da masu zanga-zanga suka kai sakatariyar jam’iyyar ta jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Litinin. Sanarwar tace jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da wasu bata-gari da suka kai hari a yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa. "Ko a ranar juma’ar da ta gabata, jam'iyyar APC ta gargadi gwamnatin jihar kan yadda ta bar wasu bata gari suna huce haushin su kan…
