24
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mambobin Jam’iyyar adawa ta PDP kimanin 4,450 sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Jihar Binuwai. Masu sauya sheƙar da suka fito ne daga ƙananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum, Logo, Kwande da kuma Ushongo sun koma APC ne a ranar Talata. Gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ne ya karɓe su a wani biki a yayin da yake gudanar da rangadin godiya ga al’ummar jihar. Gwamnan yana yin zagaye a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar ne domin nuna godiyarsa bisa goyon bayan da ya samu har ya lashe zaɓen 2023. A jawabinsa a wurin karɓar masu sauya…
