06
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai ci gaba da zama shugaban Nijeriya har bayan 2027. Ganduje ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja. Ganduje ya ƙara da cewa tun ba a kai ko'ina ba jam’iyyun adawa sun fara kermar tsoron yin gaba da gaba da APC a zaɓuka masu zuwa bayan ɗan karan kayen da suka sha a zaɓen 2923. "Jam’iyyar NNPP sun fi duk jam’iyyun kiɗimewa. Sai tsalle-tsalle suke…
