Siyasa

An kori Ganduje daga Jam’iyyar APC

An kori Ganduje daga Jam’iyyar APC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jam'iyyar APC ta mazaɓar Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta sanar da dakatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mamaba a jam'iyyar. Mai bai wa Jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje, Hon. Halliru Gwanzo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin Jihar Kano ta yi masa na karɓar cin hanci da rashawa. Ya ce dakatarwar ta fara ne daga daga ran 15…
Read More
Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH Tsigaggen Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi watsi da matakin da Majalisar Dokokin Jihar ta ɗauka na tsige shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar. Shaibu ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗan bayan da majalisar jihar ta sige shi. A ranar Litinin Majalisar Dokokin Jihar Edo ta tsige Shaibu daga muƙamin nasa bayan da ta karɓi rahoto kan binciken da aka gudanar a kansa, kana ta maye gurbinsa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo. Majalisar ta kafa…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH An naɗa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo. Naɗin nasa ya biyo bayan tsige Mataimakin Gwamnan mai barin gado, Philip Shaibu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi ne. Omobayo injiniya ne a fannin lantarki kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Akoko-Edo da ke jihar. An tsige Shaibu a muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne yayin zaman da majalisar ta yi a ranar Litinin. Majalisar ta ɗauki matakin tsige Shaibu ne bisa shawarwarin Kwamitin Binciken da ya gudana ƙarƙashin Justice S.A. Omonua-led mai murabus, binciken da aka gudanar bayan da Majalisar jihar…
Read More
Za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Ningi ba da daɗewa ba – Akpabio

Za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Ningi ba da daɗewa ba – Akpabio

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa, nan ba da daɗewa ba za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya) a Majalisar Dattawa. Ya bayyana hakan sa'ilin da yake amsa wa manema labarai tambayoyi a wajen wani taro da aka shirya ranar Juma'a a Geneva, Switzerland. Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan da Ningi ya yi wa Akpabio kan cewa zai ƙalubalanci dakatar da shi da aka yi a kotu muddin ba a janye dakatarwar ba a cikin kwana 7. An dakatar da Ningi daga majalisar ne biyo…
Read More
Jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da aƙida – Ganduje

Jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da aƙida – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dr Abdullahi Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya ce jam’iyyun siyasa a Nijeriya ba su da asali da aƙida, wanda ke haifar da sauya sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya ƙaddamar da kodinetocin jam’iyyar na shiyyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya ce dole ne lamarin ya canza da kyau. Ya ce kodinetocin shiyyar ne za su kula da shiyyoyin siyasa shida na ƙasar nan. Gwamna Ganduje ya naɗa Gwamna Hope Uzodimma na Imo a matsayin kodinetan shiyyar Kudu Maso Gabas, yayin da Gwamna…
Read More
Ko a mayar da ni nan da kwana bakwai ko mu haɗu a kotu – Sanata Ningi ga Majalisa

Ko a mayar da ni nan da kwana bakwai ko mu haɗu a kotu – Sanata Ningi ga Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Ahmed Ningi, ya rubutawa shugaban majalisar, Godswill Akpabio wasiƙa, yana neman a ɗage dakatarwar da aka yi masa. Ningi, wanda ya rubuta wa Akpabio wasiƙa ta hannun lauyansa, Femi Falana (SAN), ya bayyana cewa idan ba a ɗage dakatarwar da aka yi masa ba nan da kwanaki bakwai masu zuwa zai kai majalisar dattawa gaban babbar kotun tarayya. Majalisar dattawa, a ranar 12 ga watan Maris, ta aika wa Ningi dakatarwar watanni uku saboda iƙirarin da ya yi na cewa an yi cushe a kasafin…
Read More
Abure ya zama Shugaban Jam’iyyar Labour na Ƙasa karo na biyu

Abure ya zama Shugaban Jam’iyyar Labour na Ƙasa karo na biyu

Daga BASHIR ISAH An sake zaɓan Mr Julius Abure, a matsayin Shugaban Jam'iyyar Labour na ƙasa karo na biyu. Daliget ne suka sake bai wa Abure wannan dama ba tare da hamayya ba. An zaɓe shi ne duk da hamayya daga ɓangaren Jam'iyyar NLC. Shugaban babban taron jam'iyyar kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Abia, Mr Ikechukwu Emetu, shi ne ya ayyana Abure a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugabancin jam'iyyar wanda ya gudana ranar Laraba a Nnewi, Jihar Anambra. Kafin wannan lokacin, an kai ruwa rana tsakanin Abure da NLC ƙarƙashin jagorancin leadership Joe Ajaero. Inda NLC ta buƙaci Abure ya…
Read More
Gwamna Abba ya kama hanyar naɗa ɗan gidan Kwankwaso muƙamin kwamishina

Gwamna Abba ya kama hanyar naɗa ɗan gidan Kwankwaso muƙamin kwamishina

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf, ya aika da sunan ɗan gidan Rabi'u Kwankwaso, Mustapha Rabi’u Kwankwaso, zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa kafin naɗa shi muƙamin kwamishina a jihar. Shugaban Manalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar a ranar Talata. A cewar Falgore, sunayen da Gwamnan ya aike sun haɗa da: 1- Adamu Aliyu Kibiya2- Usman Shehu Aliyu3- Mustapha Rabiu Kwankwaso4- Abduljabbar Garko Ana sa ran waɗanda lamarin ya shafa su bayyana a gaban Majalisar a ranar Talata, 2 ga watan Afrilun 2024, don a tantance su.
Read More
Ɗan takarar Gwamnan Ondo, Dokta Akintelure ya kwanta dama

Ɗan takarar Gwamnan Ondo, Dokta Akintelure ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar gwamnan Jihar Ondo ƙarƙashin jam'iyyar APC, Dr Paul Akintelure, ya kwanta dama. An tabbatar da mutuwarsa ne da safiyar Talata, 26 ga Maris, 2024. Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata marigayi Akintelure ya yi ƙorafi kan barazanar kisa da yake fuskanta. Bayanai sun ce likitan da ya duba shi ya ce, Akintelure ya rasu ne a Legas. Kafin wannan lokaci, mai magana da yawun marigayin, Oladapo Akintelure, ya faɗa a cikin wata sanarwa da ya fitar cewar yana da yaƙinin barazanar da ake yi wa maigin nasa zai gushe. Sai dai…
Read More
Zargin cushe a kasafin 2024: Yadda dakatar da Sanata Ningi ta tada ƙura a Nijeriya

Zargin cushe a kasafin 2024: Yadda dakatar da Sanata Ningi ta tada ƙura a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A Nijeriya, jam'iyyun hamayyar ƙasar sun yi Allah-wadarai da matakin da majalisar dattawa ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku, bayan da ya yi wasu kalamai da ke nuna an cusa wasu kuɗi naira kusan tiriliyan huɗu, waɗanda ba a san inda aka nufa da su a kasafin kuɗin ƙasar na bana ba. Jam'iyyun hamayyar suna ganin kamata ya yi a fara da gudanar da bincike kan batun cushen kuɗin, don a tabbatar da gaskiya ko akasin zargin, kafin a ɗauki matakin dakatar da ɗan majalisar. Matakin dakatar da…
Read More