15
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cikin makon nan ne dai jaridar The Nation ta samu labarin cewa 'yan adawa na shirin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta tunkari jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓe mai zuwa. Gabanin shekarar 2027, majiyoyi sun ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zacen shekarar da ta gabata, Alhaji Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da ƙudirin jam’iyyar da ake son a yi tare da haɗin gwiwar wasu 'yan majalisar dokokin ƙasar. An tattaro cewa, sansanin Atiku na taka-tsan-tsan da rashin haɗin kan da ke cikin babbar jam’iyyar adawa, yana tunanin cewa idan ta…
